SHA”AWA TSAKANIN MA’AURATA
SHA"AWA TSAKANIN MA'AURATA
SHA”AWA TSAKANIN MA’AURATA
*KALMA MAI RUSA GIDAN AURE* _ME TA RASA?_
↭ _Ina mafita Ga auren mu domin Yana cikin Matsala_
• *Dan Allah yarka /yarki -danka-danki/ Ko kin taba zama dashi domin mafita Ga matsalar aure su*
*iyayeta mu sa Ido kan matsalar zamantakewar aure yaran mu*
*Gamin Gambizar Sha’awa Tsakanin Ma’aurata.*
*Assalamu Alaikum jama’a, marhabin da sake haxuwar mu a cikin wannan fili.*
InshaAllah za mu tattauna kan matsalar gamin gambizar sha’awa tsakanin ma’aurata, da fatan Allah SWT Ya sa ya amfani ma’aurata da yawa, ya kuma kawo canji na alheri cikin rayuwar auren su, amin.
Gamin gambizar sha’awa tsakanin ma’aurata wani yanayi ne da ke faruwa duk lokacin da a ka sami banbanci yanayin sha’awa tsakanin ma’aurata.
Gamin gambizar sha’awa na da qofofi da dama ta inda ta ke kunno kai cikin rayuwar ma’aurata, misali.
*in sha’awar Daya ta fi ta Daya yawa.*
*ko banbancin lokacin gabatarwa.*
*yanayin gabatarwa da kuma banbacin abubuwan yi lokacin gabatarwar.*
*Duk ta inda wannan
matsala ta Bullo, to ta kan jefa daya ko duka ma’auratan cikin wani irin hali na qunci da qaqa ni ka yi.
Mata ne su ka fi cutuwa da wannan matsalar a cikin rayuwar auren su sama da maza saboda kasancewar matsayin mace da irin
rawar da ta ke takawa cikin rayuwar aure.
In Maigida ya fi Uwargidan sa yawan buqatuwar sha’awa, dole ne ta yi ta
haquri ta na yi, mafi yawan lokaci Maigidan ma bai san irin tsananin sadaukarwa da Uwargidan sa ke yi ba wajen ba shi haqqin shi, matan aure da yawa na faxar yadda su ke Ibadar aure don kawai su fita haqqin Mazan su:
*MATSALAR MATA*
_text message Na mata_
“Tunda na yi aure ban taba jin dadin Ibadar aure ba, yanzu kusan xiya na bakwai, kuma kullum ina cikin fargabar yin shi, mi ke
kawo min haka?”
● “Ba najin sha’awa lokacin ibadar aure da miji na, ko me za mu yi ba na jin komai.” “Ina da matsala da maigida na, saboda bai yin wasa kafin ibadar aure, ni ko sai ina jin zafi, ko da yaushe ji na ke kamar ranar farko, haquri kawai na ke yi.
*Kuma ina son wasan?*
*shi ne ba ya so.*
Me ye shawara, shin in rabu da shi ne?” Haka nan in aka rashin dace Uwargida ta fi Maigidan ta buqatuwa da
sha’awa, to a nan ma wahalar ta fi yawa, domin bayan halin quncin hakan, wannan matsalar na kai wasu ga aikata ayyukan sabo garin neman mafitar sha’awar su:
● “Miji na bai damu da yin ibadar aure ba ni kuwa ga shi na kasance mai tsananin buqatatuwa da ibadar auren, in abin ya dame ni sosai na kan kalli fina-finan turawa, shin yin hakan ba laifi?” –
● “Wata ran na kan ji sha’awar miji na amma sai na kasa gaya ma shi, kuma ina cutuwa, me ye mafita?”
● “Miji na ba ya son kusanta ta da Ibadar aure,
sai mu yi wata ukku zuwa huxu kuma ni ina buqatar sa, ya zan yi dan Allah?”
● -Wata Baiwar Allah “Dan Allah sirrin rike miji ku qara kira ga maza su runqa qoqari su na biya ma matan su buqatun su lokacin ibadar aure.
Saboda ni dai ban yi dacen miji ba ta wannan fannin, ya wadatani da dukkan kayan qyale-qyalen jin dadin rayuwar duniya, amma a shekara bai fi ya kula ni sau ukku ba, na yi kuka har na gaji, na yi ma shi nasiha ba iyaka amma duk ba canji, Wallahi gab na ke da in shiga wani hali, domin ni mace ce mai tsananin buqata, ki taimake ni da shawara dan Allah?”
*TEXT NA MAZA GA MATAN SU*
● – Sannan su ma mazan su na cutuwa da shiga halin qaqa ni ka yi in Allah Ya yi matan da su ke aure ba ma su haquri ba ne balle har su daure su sadaukar da na su jin dadin don farantawa mazan su:
௹ “Duk lokacin da mu ke tare da mata ta, ba ni da ikon ta~a jikin ta sai ta ture hannu na, kuma ita har mu gama ibadar aure ba za ta ta~a jiki na ba, ba ta son ayi wasanni ko kadan, kuma ba ta jin nasiha.
Wannan abin ya na damu na, a taimaka min da shawara.”
௹ “Me ke sa wasu matan sai su runqa nuna kamar an matsa ma su duk lokacin da aka neme su, ko su fadi wata bakar maganar har mutum ya ji ya fasa?
Ya za a gane irin wadannan mata don a kauce ma su, kuma in mutum ya riga ya aura menene mafita?
Domin irin wannan ya sha kashe aure kuma a rasa dalilin mutuwar sa.”
௹ “Ina da sha’awa sosai, fahimtar haka ta sa aka yi min aure da wuri sai dai ban yi dacen mata ba, don in zan yi wata ban kula ta ba ko a jikin ta, har cika baki ta ke da hakan, duk sai in ji na tsane ta. In na neme ta, ko ta amince to ban gamsuwa, shekaran mu sha daya amma har yau ban san daxin aure ba, na taba
Kara aure amma na ga duk daya su ke, me ye mafita?”
*Hanyoyin Tafiyar da Gamin Gambizar Sha’awa*
☞ *Ko / ka taba zama domin gyaran zamantakewar aure yarka/yarki*
Zan fara gabatar da nasiha ga mazan da matan su su ka fi su bukatuwa da sha’awa.
sannan don mugunta sai su share su har sai ranar da su su ka buqace su alhali su na sane dahalin da su ke ciki na tsananin buqatuwar sha’awa, su sani wannan ba jarumta ba ce, raggwanci ne na qarshe.
Ya ku irin waxannan Magidanta, ku sani, babban jigon da a ka gina aure a kai, shi ne saduwar ibadar aure don biyan Bukatar sha’awar juna, don haka in mace ta zan ba ta iya gamsar da namiji ko namiji ya zan ba ya iya gamsar da matar sa, to wannan qwaqwqwaran dalili ne na a raba auren don ta sami wani wanda zai iya gamsar da ita.
Cikar mazantakar xa namiji shi ne ya kasance mai gamsar da iyalan sa ta ko wane irin fanni na rayuwar su amma musamman ma ta fannin ibadar aure.
Ku sani, rayin dan’adam na iya daure ma dukkanin bukatuwar rayuwar duniya, amma ban da bukatuwar ibadar aure saboda da tsananin qarfin ta da girman ta, to meye amfanin auren da
matan na ku su ke yi da ku in auren bai yi ma su maganin
tsananin bukatuwar su ta sha’awa ba?
*Sai dai su kunqa kallon kafirai su na zina don su rage zafi?*
*Ko inda mace Ce ta dinga lesbian Ko zina*
Dubi irin hadarin da ku ke tura matayen ku a ciki?
In har ku na son su don mi
ba za ku sadaukar da ko da sau daya a wata ne ba don
warkar ma su da tsananin buqatuwar su?
Wannan wane irin zalunci ne a ce ka aje lafiyayyar mace a gidan ka amma sau ukku kadai ka ke waiwayar ta a shekara?
Duk wani kayan jin dadin da za ka tanadar ma ta na banza ne tunda ga wani abu da ta fi so sama da komai, kuma ya kasance kai kadai ne za ka iya ba ta shi, amma ka hana ta! Kun sani akwai halattattun hanyoyi da dama da za ku biya ma matan ku buqatun sha’awar su ba tare da lallai sai ku kun yi ibadar auren ba, to in kuwa akwai so ai ya kamata ayi wannan sadukarwas, ku tuna in ku ne ku ke cikin hali irin wanda matan ku su ke ciki za ku so ayi mu ku haka?
A ji tsoron Allah dai! Mazantaka ba a qira, siffa ko halitta ta ke ba.
Mazantaka a qwaqwalwa ta ke, don haka in ku na tunanin ku cikakkun mazaje ne ta kowa ne fannin to haka
za ku kasance. In kuma ku na tunanin kun cika mazaje ne ta fannin biya ma matan ku buqatun masarufi kadai amma ban da bukatun su na sha’awa to hakan za ku kasance.
Kuma Ibadar aure ba biyan bukatar sha’awa ne kadai ribar ta ba, ta na sanya rahama da tausayi tsakanin ma’aurata kamar yadda ayoyin Alqur’ani mai girma su ka yi bayani.
*KU KIYAYE IYALANKU DAGA SHIGA WUTA*
_mu kyautatawa juna_
_mu tausayawa juna_
*INDA AN KAWO KARA GABAN KU IYAYE KADA KUCE ME TA RASA*