MENENE GWARGWADON YADDA MACE ZATA BAYYANA KARATU A SALLAH ? :

MENENE GWARGWADON YADDA MACE ZATA BAYYANA KARATU A SALLAH ? :MENENE GWARGWADON YADDA MACE ZATA BAYYANA KARATU A SALLAH ? : - Salaffiya

TAMBAYA TA 3097
********************
Assalamu alaikum:
Malam Barka da Aiki,

1, Wasu matan ko Kaɗan ba’a jin Muryar su Yayin Sallah, Shin menene gwargwadon yadda Ya kamata Mata Su fitar da Muryar su yayin da suke Sallar da ake bayyana Karatu ?

2, Nakan fita daga Gida zuwa kasuwa tun safe bana samun damar komawa, In nayi Wankan Juma’a tun Safe, zan samu Falalar da ake samu Kamar Wanda yayi wankan yayin Fita Masallaci ?

3, Ya Tabbata a Sunnar Annabi ﷺ yin Addu’a Yayinda Liman ya Zauna a Huɗubar Juma’a ?

Allah ya Ƙarawa Malam Lafiya da Nisan kwana.

AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

1. Kasancewar ita mace muryarta ma al’aura ce, Maluman Fiqhu sun fa’di gwargwadon yadda mace zatayi karatunta acikin raka’o’in da ake bayyana karatu. Shine gwargwadon yadda zata jiyar da kanta, ba tare da wani wanda ke kusa da ita yaji abinda take furtawa ba.

Amma maluman dake ganin cewa mace zata iya yiwa ‘yan uwanta mata limanci, sunce Idan limanci takeyi kuma mata zalla ne awurin zata iya bayyanar da karatu gwargwadon yadda zasuji su fa’idantu da zancen Allah.

2. Malamai sun ce mustahabbi ne yin addu’ar mamu alokacin da limaminsu ya kammala khutbah ta farko ya tsugunna. Kuma ana yi ne domin lalube ko kuma neman dacewa da lokacin nan na musamman wanda Annabi ﷺ yace idan mutum yayi addu’a karbabbiya ce.

Sai dai ba’a ruwaito wata addu’a kai tsaye daga Manzon Allah ﷺ ko sahabbansa wacce aka shar’anta yinta ba. Zaka iya rokon Allah game da bukatunka na duniya ko lahira. Amma ba tare da furtawa a fili ba, saboda kada ka shiga hakkin sauran masallata wadanda ke gefenka, kuma saboda ingantaccen hadisin da Manzon Allah ﷺ ya hana yin magana yayin da limami yake khutubah.

Don Qarin bayani aduba Fatawal Fiqhiyyah Al kubra na Hafiz Ahmad ibnu Hajr Al Asqalaniy (juzu’i na 1 shafi na 251-252).

3. Abinda yafi daidai da sunnah shine mutum yayi wankansa yayin da zai tafi sallar jumu’ah kamar yadda malamai suka fahimci hadisin. Annabi ﷺ cewa yayi :

“IDAN DAYANKU ZAI JE SALLAR JUMU’AH, LALLAI NE YAYI WANKA”. (Bukhariy da Muslim suka ruwaitoshi).

Wankan Jumu’ah sunnah ne mai karfi, wasu maluman ma cewa sukayi wajibi ne yinsa. Don haka idan kana da iko koda a kasuwar ne ka rika shiga toilet kana yi domin riskar falalar dake cikinsa.

Duk da dai wasu maluman sun ce wanda yayi shi tun da sassafe ba sai ya maimaita ba. Ma’ana ba’a wajabta masa maimaitawar ba.

WALLAHU A’ALAM.

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (10/04/1445 25/10/2023).