KOFAR TUBA TANA BUDE

KOFAR TUBA TANA BUDE
KOFAR TUBA TANA BUDE - Salaffiya
Duk irin laifin da kasan kayiwa Ubangiji idan har ka tuna girman ALLAH ka tuba tuba mai tsarki Ubangiji zai wanke wanan laifin tas

Wata rahama ta Ubangiji idan ka tuna irin laifin da kakeyi a baya ka tuna yadda rayuwarka ta samu sauyi a yanzu lada Ubangiji zai baka

Idan zina kakeyi ka tuba ka daina kayi hakurin tsare mutuncinka WALLAHI malam kullum ladan tasbihi za’a rubuta maka

Dan haka nake kwadaita mana tuba musanman a wannan wata mai tarin albarka
Ubangiji ka bamu ikon tuba ka amshi tuban namu

Ubangiji kasa wanan ramadan yazama sanadin chanjawar mu daga laifi zuwa tuba taubatan nasuha
Ubangiji kasa sanadin gyara aikin mu acikin wanan wata yazama tazarce daga nan har sanda zamu komo izuwa gareka.

Zauren Malam Ahmad Tijjani Yusuf Gurumtum Bauchi
Mallam Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum