SAKO DA FATAN ALHERI ZUWA GA SHUGABAN IZALA NA DUNIYA

SAKO DA FATAN ALHERI ZUWA GA SHUGABAN IZALA NA DUNIYA[/caption]

Yanzu haka birnin Bauchin Yakubu ta dau harami da dubban daruruwan Musulmi Ahlussunnah domin gudanar da wa’azin Kasa na Kungiyar Izala karkashin Jagorancin Shugaba Sheikh Dr Abdullahi Bala Lau (H)

Allah shaida ne ina kaunar Sheikh Abdullahi Bala Lau domin kasancersa Malami kuma jagora mai kishin Musulunci sannan kuma garkuwa ga Musulmin Nigeria

Tabbas ina da masaniya game da kokarin da Malam ya ke yi wajen kwatawa Musulmi hakkinsu da kare martaban Musulmin Nigeria a zahiri da kuma a sirrance

Kasancewar Malam ya zo Bauchi garin Limamin Jaddada Sunnah na Afirka Sheikh Dr Idris Abdul-Aziz Bauchi zan so ace Malam ya shiga cikin lamarin dan uwansa a sirrance kamar yadda na san ya saba da yin haka

Hakika abin kunya ne kuma abin takaici ace Malam Idris Abdul-Aziz an yi masa hari an firgitashi, an yayata nemansa ruwan a jallo alhali bai kasance barawo ko dan ta’adda ba, ba matar wani ya nema ba, ba hakkin wani yaci ba, karantarwa kawai yake yi akan tauhidi, amma sai muka ga ‘yan uwansa manyan Malamai sun ja baki sun yi shiru saboda kawai ya samu sabani da su

Duk da a wani bangare ban ga laifin Malaman ba, amma ba shakka ina so Shugaba Abdullahi Bala Lau ka san da cewa akwai wasu manyan munafukai daga cikin Malamai wadanda suke hada Malam Idris rikici da wanin da Allah Ya bashi iko na takaitaccen lokaci

Sheikh Idris Abdul-Aziz Bauchi yace bai yadda wani ya shiga cikin lamarinsa ba, amma munafukan nan su yi hakuri su dena kulla masa makirci a gurin mutumin nan da Allah Ya bashi iko na takaitaccen lokaci yake wulakantashi

Wannan na daga cikin abinda ya sa Malam Idris ya fusata yace bai yadda wani Malami ya shiga cikin rigimarsa ba wanda ni nake ganin hakan a matsayin kuskure duk da an masa ba dadi

Shugaba Abdullahi Bala Lau idan ka shiga lamarin Malam Idris to ba wai Malam Idris din ka shigarwa ba, ka shigarwa mutuncin Malamai ne ‘yan uwanka, ka shigarwa addinin Allah ne, domin Malam Idris Ahlussunnah ne dan uwanka da yake karantar da tauhidi, zakayi don Allah ne ba don shi ba

Maigirma Shugaban Izala, ka dubi girman Allah, kayi hakuri kafin ka bar Bauchi ka ziyarci Masallacin Malam Idris kayi nasiha da fadakarwa, ka dubi halin da iyalansa da marayun dake karkashinsa suke ciki ka basu hakuri, a kalla dai zasu ji dadi, ko haka kayi na tabbata ka aika da wani babban sako zuwa ga wadanda suke cutar da Malam Idris

Daga karshe ina maka fatan alheri, ina jaddada mubayi’ata a gareka, ina fatan Allah Ya sa ayi wa’azin kasa lafiya a kammala lafiya kuma a koma gida lafiya Amin