Yau Kungiyar IZALA Ta Cika Shekaru 46 Da kafuwa.

Yau Kungiyar IZALA Ta Cika Shekaru 46 Da kafuwa.

Yau Kungiyar IZALA Ta Cika Shekaru 46 Da kafuwa.
Yau Kungiyar IZALA Ta Cika Shekaru 46 Da kafuwa. - Salaffiya
A Rana mai Kamar Ta Yau 12 Ga Watan Maris 1978 Aka Kafa Kungiyar Jama’atu Izalatul Bidi’a Wa’Ikamatus Sunnah (JIBWIS).

JIBWIS Ƙungiyar Addinin Musulunci ce, mabiya Sunnar Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi. Sannan kuma an kafa wannan ƙungiyar ne a babban Birnin Jihar Plato dake Jos wanda babban malamin Musulunci kuma Babban Hafsan Sojan Najeriya ya kafa, wato Sheikh Ismaila Idris Bin Zakariyya Jos wanda kuma har yanzu Cibiyar Gudanarwa na kungiyar yana garin Jos a karkashin jagorancin Khalifa na farko na wannan ƙungiya wato Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir.

Daga cikin muhimman manufofin wannan ƙungiya sun hada da:

(1)- Kaɗaita Allah da bauta ba tare da haɗa Shi da wani ba (shirka). Sannan a tabbatar da biyayya ga Annabi Muhammadu (S.A.W) ba tare da jayayya ko kawo maganganun wasu mutane na daban ba.

(2)- Tabbatar da bin ɗabi’un (sunna) Manzon Allah (S.A.W) ba tare da ƙirƙire-ƙirƙire ba.

(3)- Watsi da dukkan al’adun da suka saɓa ma addinin Islama.

(4)- Soyayyar Annabi (S.A.W) da iyalan shi da sahaban shi /abokan shi da kuma surukan shi ba tare da sukar ko ɗaya daga cikinsu ba.

(5)- Tabbatar da neman ilimin addini da na boko a ko’ina a faɗin duniya tare da bin dokokin addini.

(6)- Tabbatar da mutuncin waliyyan Allah na gaskiya da salihan bayi da duk sauran mutanen kirki. (Wikipedia)

Yau Shekaru 45 daidai da kafa kungiyar Izala wadda Sheikh Ismail Idris Bn Zakariya ya kafa ta a garin Jos, kuma ya jagorance ta har zuwa karshen rayuwarsa.

Malam ya sha gwagwarmaya da makiya sunnah a wancan lokacin, har yunkuri kashe shi an yi, ya je gidan yari a sanadiyyar wa’azi.

An taba kama Sheik a garin Kano daga can aka wuce da shi Cross River (Calabar) sai da ya yi kwana 40 ba a san inda yake ba.

Saboda wa’azi Sheik ya bar aikin soja. An sha fama sosai wanda wani garin ma idan suka je wa’azi aka hana su, misali wata rana an je wa’azin kasa Maiduguri, ana dab da shiga garin Maiduguri domin wa’azi sai aka ce ba za a shiga ba, Sarki ya hana duk cewa a wancan lokacin sai an nemi izini a wajen hukuma kafin zuwan su amma duk da hakan aka hana su karshe dai Sheikh ya bawa jama’a hakuri aka koma gida.

Sheikh ya yi rayuwa abin koyi da burgewa a matsayin sa na Malamin addinin Musulunci. Duk girman ka Mal zai fada maka gaskiya ba tare da tsoro ba.

Allah muke roko da ya lullube shi da rahmar sa, Ya sa ya huta idan ta mu ta zo Ya sa mu cika da Imani.

Rubutawa Saliadden Sicey.