Murabus Ɗin Malam Aminu Daurawa Daga Hukumar Hisba Ta Kano

Murabus Ɗin Malam Aminu Daurawa Daga Hukumar Hisba Ta Kano[/caption]

Muna alhini da rashin jin daɗin abin da ya faru na murabus ɗin Malam Aminu Daurawa daga jagorancin hukumar Hisba ta kana. Wannan ba ƙaramin abun takaici da ɓacin rai bane, ace an ajiye Malamai an ɗauki mutanen banza marasa tarbiyya (Ƴan Tiktok) an goyi bayan su cigaba da fitsara da rashin kunya ana kallon su.

Muna yabawa Malam bisa ƙoƙarin da yayi a wannan aiki da aka bashi na tsawon lokaci, abubuwan da yayi na dai-dai Allah ya karɓa masa, kusakuren shi kuma Allah ya yafe masa.

Ku kuma mutane ya kamata ku ƙara gane ƴan siyasa da kyau. Ku gane cewa waɗannan ƴan siyasar namu babu abin da ya dame su sai siyasar su, babu addini a gaban su.

Kuma a gefe guda zuwa dakai ya fi saƙo dole mutanen kirki su shiga siyasa domin kawar da ɓarnar da kuma kuɓutar da al’umma daga irin wannan baƙin mulki na zalunci ake yiwa al’umma a wannan ƙasa baki ɗaya, wanda haka shi ya janyo aka gurɓatawa al’umma rayuwar su ta nan , kuma gashi lahirar ma ana so a gurɓata mana ita ta hanyar turo mana waɗannan mara sa kunya fitsararru (Ƴan Tiktok) da kuma fifita su sama da mutanen kirki.

✍Dr. Suleiman Mahmud Al-Azhary
1/3/2024