SHAWARA GAREKU ‘YAN MATA

SHAWARA GAREKU ‘YAN MATASHAWARA GAREKU 'YAN MATA - Salaffiya

1- Kada ka jira har sai an bukaci ka turo, kaine za ka fara neman izinin tura magabatanka, daga nan idan an amince maka sai ka tura, idan ba’a amince ba, ka sake neman izini a karo na biyu da na uku, wannan shi zai tabbatarwa da iyayenta hakika dagaske auren yarsu kake nema, ba yaudara ta kawoka ba!

2- Kada ka jira sai wadda kake so ta kira ka a waya, kayi ta kiranta ba tare da neman biyan bashin kira daga gareta ba, idan har tana amsa wayar, kuma ta saki jiki tare da baka lokacinta kuyi fira sosai, wannan kadai ya wadatar dakai,

3- Shashanci ne duk bayan kwana 2/3 a dinga ganinka a kofar gidan su yarinya, idan kana son ka kankarowa kanka mutunci sannan a dinga daukin zuwanka to mafi kusa zuwanka ya kasance duk bayan kwana 10 ko kuma sati 2,

4- Babu laifi ka dinga kiranta a dare da safiyar kowacce rana, amman son samu kiran safe tsayin maganar kada ya haura minti 2, amman kiran dare idan kana da dama har tsawon minti 30 zaku iya shafewa kuna waya,

5- Kada ka dinga shafe watanni 2 kana soyayya da yarinya, amman a cikin wata biyun nan ba ka shiga cikin gidansu ko sau daya domin ka gaisa da mahaifiyar ta,

6- Na haneka da yin soyayyar littafi ko kuma ta film ga wadda kake neman aurenta, idan kuwa kace irin wannan soyayyar zaka nuna mata, ina mai tabbatar maka kwabarka za tayi ruwa!

A karshe zan sake maimaita maka abinda na ambata maka a farko saboda muhimmancin sa, kada ka jira sai iyayen wadda kake so su ce ka turo, kaine zaka fara sanar da ita ta sanar a gida kana son ka turo, duk abinda aka fada mata ita kuma zata sanar dakai, daganan sai kayi abinda ya dace.

Zaka iya daukar lokaci me tsayi kana soyayya da yarinya, a zuciyarta tana son ka turo, amman kunya ta hana ta iya fada maka, a wannan lokacin kuma idan aka samu wani saurayin wanda ya fika zafin nama shima yana sonta, kawai sai ya tura nasa iyayen, daganan kuma sai labarin ya canza, domin ba zasu ki karɓar maganar sa ba, tunda dai baka

Salaffiya ✍️