SABANI BA HUJJA BANE NA KIYAYYA DA NUNA GABA GA JUNA.

SABANI BA HUJJA BANE NA KIYAYYA DA NUNA GABA GA JUNA.SABANI BA HUJJA BANE NA KIYAYYA DA NUNA GABA GA JUNA. - Salaffiya

Bara mu falsafe.

Wanin ku shinkafa yaci, waninku kuma Taliya yaci, waninku kuma garin kwaki yaci, a yayin da waninku kuma tuwo yaci, amma abin muradi shine gusar da yunwa.

Wani duk duniya babu abincin da yafi soyuwa gareshi sama da shinkafa, a yayin da wasu kuma sabaninsa kamar Taliya, Garri ko tuwo da sauransu, su ne abinci mafiya soyuwa gare su.

ABIN LURA ANAN SHINE.

Saboda kai shinkafa shi ne abinci mafi soyuwa gareka, kawai sai kace: Duk wanda yaci wani abinci sabaninsa sam ba abinci yaci ba, kuma ba zai gusar masa da yunwa ba? Ashe dai kowa da nasa zabin, da kuma abinda yafi jan hankalinsa kuma yake gusar masa da yunwa.

SABODA HAKA

Idan ka zabi Izalanci a matsayin minhajinka da kake burin samun tsira, to kada kake tsangwama da ta’azzarawa wanda ya riki tafarkin Sufanci a matsayin tafarkin da shi kuma ya zaba a matsayin Minahjinsa da yake burin samun tsira Duniya da Lahira.

MAI YIWUWA ABINDA KAI YAKE GUSAR DA YUNWARKA, GA WANI KUMA SHI YAKE TAYAR MASA DA ITA, ASHE KENAN KOWA YA FUSKANCI MAFUSKANTARSA, BA TARE CIN FUSKA KO CIN MUTUMCIN MAFUSKANTAR WANINSA BA.

ALLAH BAMU IKON KIYAYEWA.

 

Salaffiya ✍️