Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa Ikamatis Sunnah ta Kasa ta gabatar da taron Majalisar ta Kasa a Birnin Katsina a ranar Asabar 21-10-2023 a dakin taro na Ma’aikatar Kula da Kananan Hukumomi da ke kan hanyar zuwa Kaita

 

Kungiyar Jama'atu Izalatil Bidi'a Wa Ikamatis Sunnah ta Kasa ta gabatar da taron Majalisar ta Kasa a Birnin Katsina a ranar Asabar 21-10-2023 a dakin taro na Ma'aikatar Kula da Kananan Hukumomi da ke kan hanyar zuwa Kaita - Salaffiya

Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa Ikamatis Sunnah ta Kasa ta gabatar da taron Majalisar ta Kasa a Birnin Katsina a ranar Asabar 21-10-2023 a dakin taro na Ma’aikatar Kula da Kananan Hukumomi da ke kan hanyar zuwa Kaita

Taron ya kasance ne bisa jagoranci Shugaban Kungiyar na Kasa (Dr.) Sheikh Abdullahi Bala Lau. Wanda yayin taron ne Shugaban ya mika takardun kama aiki ga Shuwagabannin Kwamitocin da aka nada a yayin taron da Kungiyar ta gabatar a Garin Hadejia

1. Kwamitin Kula da Marayun Masu Da’awa, Shugaban JIBWIS Sheikh Abdullahi Bala Lau zai jagoranta da Kansa wato (Chairman Board of Directors), Mataimakin Shugaban Kwamitin – Sheikh Dr. Ibrahim Jalo, Sakataren Kwamitin Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe

Mambobin Kwamitin:
i. Sheikh Yakubu Musa Hassan
ii. Sheikh farfesa Mansur Ibrahim Sokoto
iii. Alhaji Auwal Rano (A.A. RANO)
iv. Tsohon ministan sufuri Alhaji Mu’azu
v. Alhaji Auwalu Lawan Gombe
vi. Alhaji Ibrahim Katsina
vii. Alhaji Sani Sambo Lagos
viii. Daraktan Agaji Mustapha Imam Sitti

Management na wannan Kwamiti, Sheikh Ibrahim Sabi’u Jibia shi zai kula da kwamitin a dukkan mataimakai, Dr. Fa’iz Bashir kuma shine Sakataren kwamiti.

2. Daraktan Kwamitin Masallatai – Sheikh Dr. Ibrahim Jalo Jalingo, Sakataren Kwamitin Dr. Salisu Barau

3. Shugaban Kwamitin Ayyuka – Sheikh Habibu Yahaya Kaura, Mataimakin Shugaban Kwamitin – Ramalan Azare, Sakataren Kwamitin Sheikh Ibrahim Idris Darus-Sa’ada

4. Shugaban Kwamitin Walwala – Sheikh Dr. Isma’ila kumo

5. Mataimakin Kwamitin Da’awa – Sheikh Umar Jega, Sakataren Kwamitin Sheikh Dr. Jameelu Zarewa

6. Kwamitin Ilimi mai zurfi (Higher Education) – Sheikh Professor Abdullahi Sale Pakistan, Sakataren Kwamitin Sheikh Dr. Magaji Fadlu Zarewa

7. Kwamitin ilimi da ilimantarwa (Basic Education) – Sheikh Dr. Ibrahim Abdullahi R/lemo, Sakataren Kwamitin Malam Usman Alhaji Sale Potiskum

8. Shugaban Kwamitin Seminar – Sheikh Abubakar Abdussalam Baban Gwale, Sakataren Kwamitin Sheikh Saifuddeen Yakubu Musa

9. Shugaban Kwamitin Marayu – Alh. Usman Ibrahim Yola, Mataimakin Shugaban Kwamitin – Alhaji Abdullahi Abdulmalik Diggi, Sakataren Kwamitin Dr. Malami Garba

JIBWIS NIGERIA