Kwamitin Nisa’ussunnah wadda take karkashin Kungiyar JIBWIS ta Jihar Gombe ta gabatar da shiri na tallafawa Iyaye Mata wadanda suke rike da Marayu guda 500.

  • Kwamitin Nisa’ussunnah wadda take karkashin Kungiyar JIBWIS ta Jihar Gombe ta gabatar da shiri na tallafawa Iyaye Mata wadanda suke rike da Marayu guda 500.Kwamitin Nisa'ussunnah wadda take karkashin Kungiyar JIBWIS ta Jihar Gombe ta gabatar da shiri na tallafawa Iyaye Mata wadanda suke rike da Marayu guda 500. - Salaffiya

Daga Musa H Musa.

A yau Lahadi Kwamitin Nisa’ussunnah ta karamar Hukumar Gombe ta kaddamar da tallafawa Iyayen Marayu guda 500 da kudi Naira dubu 10,000 ga kowace mata domin taja jari, taron ya gudana a filin Marayu dake Unguwar Bolari bayan sakateriyar Kungiyar JIBWIS ta Jihar Gombe.

Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe shine babban bako mai jawabi ya janyo hankalin iyaye mata da maida hankali wajen bayar da tarbiyya ga ya’ya da Allah ya azurtasu da su domin hakkine da Allah zai tambaya. Tare da ambata falalan kula da marayu. Sannan Shehin ya tallafawa Asusun ginin Makaranta na marayu da kudi Naira Dubu Dari.

Shugaban Kungiyar JIBWIS ta Jihar Gombe Alhaji Salisu Muhammad Gombe ya bayyana wannan aiki na kwamitin Nisa’ussunnah a matsayin gagarumin aiki wadda shine ake bukata a wanann yanayi da ake ciki domin tallafawa marayu da wadanda suke rike dasu.

A nata jawabin Babbar Joji ta Jihar Gombe Hajiya Halima S. Muhammad tayi kira ga Iyaye mata da su kasance masu kula da marayu domin suma Allah zai kula da nasu bayan basa nan su kuma Jajirce wajen bawa ƴaƴansu tarbiyya.

Shugaban Karamar Hukumar Gombe Alhaji Ali Ashaka ya yi kira ga Al’umma dasu kula da yaransu su kuma mika rahoton bata gari domin daukan matakin a unguwanni

Taron yasamu halartan Shuwagabannin kungiya da Malamai da Sarakuna da iyayen Marayu, Muna addu’ar Allah ya shiga cikin lamuran shuwagabannin mu baki daya.

JIBWIS Gombe
Social Media Directorate.