SHAIDA NA SADAUKAR DA MILIYAN 383 GA FALASDINAWA KU

SHAIDA NA SADAUKAR DA MILIYAN 383 GA FALASDINAWA KUSHAIDA NA SADAUKAR DA MILIYAN 383 GA FALASDINAWA KU - Salaffiya

Kai tsaye daga wajen lakcar da Dr Zakir Naik yake gabatarwa yanzu haka a Sokoto yace, wasu yan siyasa guda biyar sun ɓata min suna, kuma na shigar dasu kara a kotu. Mun sasanta da huɗu daga cikin su, amma na biyar ɗin kam na ki amincewa mu sasanta.

Bayan tsawon lokaci ana Shari’a, yau da safe, 2 ga watan November, an yanke hukunci. Alkali ya umarce shi da ya biya ni kuɗi akan ɓata min suna da yayi, kuɗin idan an canza su zuwa kudin Nigeria, suna dai dai da Naira Miliyan 383.
Ku shaida na sadaukar da kudin ga Falasɗinawa. Ba na buƙatan ko sisi a ciki!

Bawan Allah, Allah ya biya ka, ya karba maka ayyukan ka, ya ‘kara daukaka fiye da yadda Makiya suke zaton ka kai.

#Salaffiya ✍️ Salaffiya