DANGANE DA MUQABALAR DA AKA SO AYI YAU A GARIN BAUCHI.

DANGANE DA MUQABALAR DA AKA SO AYI YAU A GARIN BAUCHI.

Dan tsokaci na akan hakan, ya kamata jama’ah su fahimci abubuwa kamar haka:-

Abu na farko tinda masu son yin muqabalar suka neme shi da yin muqabalar tuni ya ce suzo su sameshi a masallacinsa ayi.

Kuma ya bada misalan cewa ya yi muqabaloli da mutane mabanbanta kuma a Masallacin nasa ba tare da anci zarafin kowa ba.

To amma sai aka samu akasi wadanda zasuyi muqabalar da shi ba suyi tsare-tsaren komai da shi ba.

Su kadai suka yi tsare-tsarensu ba tare da shi ko wakilansa ba, wadda da a wajan tsare-tsaren ya kamata ace an tintibe shi.

Sune suka saka rana ba tare da shawararsa ba, sune suka zabi wajan yi ba tare da amincewarsa ba, hatta abin da za’a tatattuna akai su suka za’ba ba tare da jin ta ‘bangarensa ba.

Idan za’a masa adalci ya kamata ayi magana da shi, Saboda haka babu maganar adalci ko kadan a abin da aka yi masa.

Kuma mu tuni muna tare da Dr. Idris Abdul’azeez indai akan abin da za’a tatattuna ne, saboda shi Sunnah yake son tabbatarwa da bata kariya.

Su kuma gayyar masu muqabalar da shi Qungiyarsu, da son zuciyarsu hadi da goyan baya magabatansu akan abin suke karewa ba Sunnah ba a fahimtarmu.

Nayi wannan rubutu ne domin fadar ra’ayi na, da fahimtata akan abin kasancewar ina da ‘yancin yin hakan kamar yadda naga wasu daga cikinsu sunata rubutu wai Dr. Idris Abdul’azeez yaji tsoro ya kasa zuwa.

Kar mai karatu ya manta ni Dan Izalar Kaduna ne, amma ina tare da duk wadda na fahimci yana da gaskiya a kowanna irin al’amari.

Bani da wata ala’ka da Dr. Idris Abdul’azeez data wuce goyan bayan gaskiya, wannan shi ne gaskiyar batu ba wani kwana-kwana ko kewaye-kewaye.

Kuma kar kuga irin dandazon da akayi ana jiransa, yadda kasan wa’azin ‘kasa za’a kana tinanin idan ya ‘kuresu zaisha lafiya a gun

Allah muke roko ya tabbatar da mu akan daidai, ya bamu ikon gyara inda muke da kuskure kasancewa zamu iya daidai a wani waje, za kuma mu iya kuskure.

Ameeeen Yah Hayyuh Yah Qayyum

✍️Salaffiya