AN BUƊE ASUSUN RAMADAN NA MARAYUN MU’AZ BN JABAL FOUNDATION 1445/2024

*AN BUƊE ASUSUN RAMADAN NA MARAYUN MU’AZ BN JABAL FOUNDATION 1445/2024*
AN BUƊE ASUSUN RAMADAN NA MARAYUN MU'AZ BN JABAL FOUNDATION 1445/2024 - Salaffiya
Cikin taimakon Allah a ranar 12 Rabi’u al-Akhir, 1445 (27/10/2023) shi ne ranar da muka buɗe wannan asusun tallafin Ramadan na Marayu kimanin ɗari uku da suke karƙashin wannan gidauniya.

Kamar yadda aka sani duk shekara muna bude wannan asusu ne idan ya rage sati ashirin (20) mu shiga watan Ramadan saboda mu samu saukin taimaka waɗannan marayu da iyayen su da abin da zasu ci kuma su yi sutura kamar yanda sauran musulmi suke yi.

A duk sati zamu rinka tuna muku da wannan gidauniya mai tarin albarka, in shaa Allahu Ta’ala.

Bamu sani ba ko da mu za a yi azumin wannan shekara, amma zamu iya miƙa hannuwanmu ta hanyar bayar da gudunmuwarmu tun yanzu.

Account name: MU’AZ BN JABAL FOUNDATION
Account number: 0026264944
Bank name: Stanbic IBTC Bank

Ko

Account name: MU’AZ BN JABAL FOUNDATION
Account number: 2034569838
Bank name: First Bank

Ko a tuntubi:
Umar Shehu Zaria
Ameer
08062710092

Jamilu Mu’az Shu’aib
Secretary-general
07039122841