DAGA YAU NIMA NA ZAMA ‘YAR IZALA!!!

DAGA YAU NIMA NA ZAMA ‘YAR IZALA!!!

DAGA YAU NIMA NA ZAMA 'YAR IZALA!!! - Salaffiya
DAGA YAU NIMA NA ZAMA ‘YAR IZALA!!!

~Cewar: Wadda Aka Tsinci Kudin Ta.

Bayan ya tsinci jakar mai dauke da makuden kudaden kasar waje da kimar su ta fi naira miliyan dari (100,000,000).

Ya adanata, ya ba da cigiya, har suka hadu da mai ita, bai taba ba, bai nemi a ba shi koda tukuici ba, da aka ba shin din ma sai ya ce: NA YI NE DON ALLAH!

Sai kuwa Allah Ya nuna masa girmansa da arzikin sa.

“Duk wanda ya ji tsoron Allah to kuwa zai ba shi mafita kuma ya azurta shi ta inda bai tsammani.”

1- Kujerar Hajj = daga Jibwis
2- Naira miliyan biyu (2,000,000) daga wani dan majalisar tarayya.
3- Mota Bus daga Gwamnan Bauchi

Uwa uba, wannan mata da yar dariqa ce, a yadda aka ce, ta ce: Duk duniya ba wadanda ta tsana kafin faruwar haka kamar Shugaba Bala Lau, da Sheikh Kabiru Gombe.

Amma da ta tanbayi wannan yaro cewa Allah Ya sa dai kai ba dan Izala ba ne, sai ya ce: ai a Izalar ma ni dan a gaji ne, sai hawaye, sannan ta ce”

“DAGA YAU NIMA NA ZAMA YAR IZALA”

Manzon Allah Ya ce: Allah Ya shiryi mutum guda ta sanadin ka ya fi a baka jajayen rakuman duniya duka.

ALLAHU AKBAR, Allah mai kyauta da qari

Wannan ita ce tarbiyar da Izala ke kira zuwa gareta, tarbiyar bin tafarkin sunna.

DUBI ALKHAIRI HAWA-HAWA, duk sakamakon yin abin da Allah Ya ke so, kuma don neman yardarsa.

Allah Ya sa albarka Ya kai dan uwa ya sa sanadin arzikin duniya da lahira ne gareka da danginka.

GASKIYA DA RIKON AMANA

✍️Dr. Magaji F Ishaq Zarewa

Abdulkarim A Daudawa
23-08-1445
03-03-2024