YADDA AKE NEMAN AURE DA KULLA SHI

YADDA AKE NEMAN AURE DA KULLA SHI
YADDA AKE NEMAN AURE DA KULLA SHI - Salaffiya
Idan NAMIJI ya ji yana kaunar wata mace, kuma yana son ta da aure, to ya halattaya kalle ta yadda ya dace, don tabbatar da abin da ya yi niyya, idan Allah (SAW) yayarda.Wannan gani da zai yi mata, musulunci ya halatta masa, tun da gani ne na nemantabbatar da alheri bana barna ba, bayan samun izinin waliyyanta, bayan ya ganta,sun zanta sun amince da juna, to haramun ne kuma wani ya yi kundumbala ya shigo,saboda fadin Annabi (SAW):”KA DA WANI YA YI NEMAN AURE AKAN NEMAN DAN UWANSA, HAR SAI YABARI (idan ba a samu amincewa ba), KO KUMA SAI MAI NEMAN YA BA SHI IZINI(Idan ya ga kamar ba zai kai labari ba)” [Nasa’i 6/73 don karin bayani duba littafin ALWAJIZ 281-282]. Amma idan manemin mutumin banza ne, malamai sun yi bayanin cewa ya halattaa wargaza shirinsa.Idan namiji zai yi zance da mace, to a kiyaye wadannan sharudda:

(1.Kada ya kebanta da ita a wani wuri na daban, ya zama na suna tare damuharransa mata, ko kuma nata maza don kar su yi barna.
(2.Kada ya yi mata kallon jin dadi ka na sha’awa.
(3.Kada yayi hannu da ita, ko ya taba jikinta, don bata halatta masa ba, har sai andaura aure.
(4.Ya zama da kyakkyawar niyyar zai aure ta ne.
(5.Ya halatta ya yi zance da ita, ya tambaye ta, ta tambaye shi, abinda ya dace,don su fahimci juna, don kar a yi aure, daga baya a zo ana dan da na sani.
(6Kada ya fita da ita yawo, ko shakatawa, ko da an yi masa alkawari, yinharamunne, ko da kuwa babu abinda zai faru, fita da ita bai halatta masa ba, har saian yi aure (Baiko fa ba aure ba ne tun da ana iya warware alkawarin saboda wanidalili, don haka sai a yi a hankali).duba (FIQHUS SUNNAH LINNISA’I na Abu Malik da BAIKO BA AURE BA NE naMal. Ahmad Murtala Kano).Da za a kiyaye wadannan sharrudan, da za a samu natsuwa da jin dadi, rashinkiyaye su ne ya haifar mana da abubuwan takaici da ‘ya’yan shegu marasa asali.

Idan abubuwa sun daidaita, sai batun daura aure tare da kiyaye wadannansharrudan:

•✍️ Salaffiya