A DAINA ZALUNCI, SABODA A CECI KASA

 

 

A DAINA ZALUNCI, SABODA A CECI KASA - SalaffiyaA DAINA ZALUNCI, SABODA A CECI KASA

Bimillahir Rahmanir Raheem. Wasallahu alan Naviyil Kareem.
Idan ba a daina ZALUNCI ba Kasar nan tamu toh akwai mummunan hadari a gabanmu.

Mu da magabatanmu an ilmamtar da mu a ingantattun makarantu na Gwamnati a shekarun 1970s alhali muna ‘ya’yan talakawa, yanzu mun tabbatar da tsare-tsaren shugabanci da rayuwa na ZALUNCI wanda ke ci gaba da hana ‘ya’yan talakawa irinmu samun ilimi mai inganci. Harta makarantun Islamiyya masu inganci talaka ba zai iya shigar da dansa ba .

Idan ba a fahimci hatsarin da nake cewa muna fuskanta ba, to a kalli abin da ke faruwa gameda matasan da suka dauki makami a cikin daji suna kidnapping suna karbar kudin fansa, KO kuma su karbi kudin fansar kuma su kashe wanda suka kama.

Hakikanin abin da ya shigar da wadannan matsan na daji suka fada wannan yanayi, KO da kuwa akwai wadansu dalilan, amma hakikanin abin da ya jefasu cikin wannan mummunan aiki shi ne jahilci. An barsu cikin jahilcin ilimin addini da na boko.

Irin wannan yanayin ne muke ta ginawa a cikin biranenmu. Muna ta jahiltar da ‘ya’yan talakawa. Duk makarantun Gwamnati ba rushewa kawai suka yi ba, mutuwa murus suka yi. Makarantun nan na Gwamnati babu abin da ya rage a cikinsu face buzunsu.

Miliyoyin yaran talakawa suna tashi cikin jahilci. Babu ilimi babu sana’a. Babu addini babu adila. Kullum kuma adadinsu karuwa yake, kuma yanayin rayuwarsu kara munana yake.

Wanda duk ya dauka cewa wannan yanayin daidai ne yana cikin rayuwa ta yaudarar kai. Wanda duk ya dauka wannan yanayin zai haifar da makoma mai kyau a kasar nan, toh yana cikin rayuwa ta rudin kai. Allah Ya kiyaye lokacin da matsan birane da muka jahiltar za su dauki makamai kamar yanda matasan da muka jahiltar a daji suka yi. Idan haka ta faru , Allah ne kawai Ya san yanda makomar rayuwa a Kasarmu za ta kasance.

Muna daukar ‘ya’yanmu a motoci da babura muna kaisu makarantu na kudi wadanda suke kwas-kwas. Muna wuce ‘ya’yan talakawa suna tafiya munana ka rusassun makarantunsu, kuma muna zaton wannan ‘gwalo’ da muke musu baya haifar da zilimi da mummunan tinani a zukatansu? Wadansu yaran ma muna wucesu da ‘ya’yanmu ne a mota su kuma suna bara.Duk za mu mutu mu bar ‘ya’yanmu da muke kaisu makarantu a mota tare da ‘ya’yan talakawan da muke jahiltarwa. Su ne abokan rayuwarsu ba mu ba. Karen bana kuwa, shi ne maganin zomon bana.

Hana wani, hana kai. Ni a ganina wallahi bama tausayin ‘ya’yanmu da muke shagwabawa. Domin kuwa da wadannan ‘ya’yan talakawan da ake zalunta za su rayu. Allah Ya tsaremu daga mummunar makoma.

Muna kira ga junamu- shugabannimu, sarakunanmu masu alfarma da martaba, malamanmu masu girma da daraja, wallahi mu tashi da gaske mu yi kokarin gyara wannan yanayi don mu ceci makomar kasarmu, amma kuma musamman makomar ‘ya’yanmu da jikokinmu. Allah Ya bamu iko.

Idan an ki ji, ba a ki gani ba.

{ یَـٰقَوۡمِ لَكُمُ ٱلۡمُلۡكُ ٱلۡیَوۡمَ ظَـٰهِرِینَ فِی ٱلۡأَرۡضِ فَمَن یَنصُرُنَا مِنۢ بَأۡسِ ٱللَّهِ إِن جَاۤءَنَاۚ قَالَ فِرۡعَوۡنُ مَاۤ أُرِیكُمۡ إِلَّا مَاۤ أَرَىٰ وَمَاۤ أَهۡدِیكُمۡ إِلَّا سَبِیلَ ٱلرَّشَادِ (29) وَقَالَ ٱلَّذِیۤ ءَامَنَ یَـٰقَوۡمِ إِنِّیۤ أَخَافُ عَلَیۡكُم مِّثۡلَ یَوۡمِ ٱلۡأَحۡزَابِ (30) مِثۡلَ دَأۡبِ قَوۡمِ نُوحࣲ وَعَادࣲ وَثَمُودَ وَٱلَّذِینَ مِنۢ بَعۡدِهِمۡۚ وَمَا ٱللَّهُ یُرِیدُ ظُلۡمࣰا لِّلۡعِبَادِ (31) وَیَـٰقَوۡمِ إِنِّیۤ أَخَافُ عَلَیۡكُمۡ یَوۡمَ ٱلتَّنَادِ (32) یَوۡمَ تُوَلُّونَ مُدۡبِرِینَ مَا لَكُم مِّنَ ٱللَّهِ مِنۡ عَاصِمࣲۗ وَمَن یُضۡلِلِ ٱللَّهُ فَمَا لَهُۥ مِنۡ هَادࣲ (33) }
[Surah Ghāfir: 29-33]

{ وَقَالَ ٱلَّذِیۤ ءَامَنَ یَـٰقَوۡمِ ٱتَّبِعُونِ أَهۡدِكُمۡ سَبِیلَ ٱلرَّشَادِ (38) یَـٰقَوۡمِ إِنَّمَا هَـٰذِهِ ٱلۡحَیَوٰةُ ٱلدُّنۡیَا مَتَـٰعࣱ وَإِنَّ ٱلۡـَٔاخِرَةَ هِیَ دَارُ ٱلۡقَرَارِ (39) مَنۡ عَمِلَ سَیِّئَةࣰ فَلَا یُجۡزَىٰۤ إِلَّا مِثۡلَهَاۖ وَمَنۡ عَمِلَ صَـٰلِحࣰا مِّن ذَكَرٍ أَوۡ أُنثَىٰ وَهُوَ مُؤۡمِنࣱ فَأُو۟لَـٰۤىِٕكَ یَدۡخُلُونَ ٱلۡجَنَّةَ یُرۡزَقُونَ فِیهَا بِغَیۡرِ حِسَابࣲ (40) }
[Surah Ghāfir: 38-40]

{ فَسَتَذۡكُرُونَ مَاۤ أَقُولُ لَكُمۡۚ وَأُفَوِّضُ أَمۡرِیۤ إِلَى ٱللَّهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ بَصِیرُۢ بِٱلۡعِبَادِ }
[Surah Ghāfir: 44]

Alhamdulillah. Wassatu wassalamu ala Rasulillah.
Prof. Salisu Shehu.