YADDA AKE YIN WANKAN JANABA

YADDA AKE YIN WANKAN JANABAYADDA AKE YIN WANKAN JANABA - Salaffiya

Da farko dai ita Janaba itace fitar maniyyi daga jikin dan adam mace ko namiji, baligi ta hanyar saduwa tsakanin mata da miji, ko ta hanyar mafarki, koda yake wanka yana wajaba ga ma’aurata idan suka sadu da juna hashafa ta boya a cikin farji, koda basu yi inzali ba.

To da farko idan mutum janaba tasame shi zai yi wanka sai ya sami ruwa mai tsarki irin wanda aka siffata a baya sai ya wanke gabansa sosai, yadda ba zai sake bukatuwa ya zuwa sake wankeshi ba, sannan sai ya wanke gabban alwala sau dai-dai, in yaso ya wanke har kafafuwansa, in yaso kuma ya barsu sai a karshen wanka.

Ya kula a wajen shafar kunne ya wankeshi sosai. Sannan sai ya jika tafukan hannunsa biyu da ruwa ya murza gashin kansa dasu ance hikimar haka shine, lokacin da janaba ta sami mutum kofofin gashinsa duka sai su bude.

Don haka ba’aso kai tsaye a zuba ruwa akan amma idan aka murza kan sai kofofin gashin su rufe, domin rashin yin hakan zai iya cutar da lafiyarsa.

Sannan ya kamfato ruwa da hannuwansa ya wanke kansa sau uku mace ma haka zatayi, ta murza gashin kanta ta wankeshi sosai, amma ba sai ta kwance kitsonta ba, sai dai idan daure-daure tayi to wannan lallai ne ta kwanceshi.

Sannan sai ya wanke tsagin jikinsa na dama tun daga kafada har zuwa idan sawu, sai kuma ya wanke tsagin jikinsa na hagu, tare da cuccudawa ya tabbatar ya wanke ko’ina.

Wanda hannuwansa basa iya wanke bayansa to yai amfani da hankici ko wani abu mai kama dashi, dan ya tabbatar ya wanke bayansa tare da cuccudawa, an so ya bibiyi kwarin cibiyarsa da kasan makogwaronsa ya tsetstsefe gashin gemunsa, ya sabunta wanke hammatarsa, da tsakanin mazaunansa da kwarin guiwowinsa, ya tsetstsefe ‘yan yatsun hannuwansa ya wanke kafafuwansa.

Lallai ya kula duk inda gashi yake a jikinsa ya tabbatar ya cuccuda ya wankeshi sosai, saboda a karkashin kowane gashi akwai janaba.

Wanda ya zama ya gabatar da alwala tun da fari to ya kula karya taba azzakarinsa da tafin hannuwansa don kada alwalarsa ta warware.

•✍️ Salaffiya #Salaffiya