Sheikh Yusuf Sambo Yake Fadi Mana Cewa; Wasu abubuwa ma wa’azi guda suka faru a gabansa ba wai labari ba.

Sheikh Yusuf Sambo Yake Fadi Mana Cewa;

Wasu abubuwa ma wa’azi guda suka faru a gabansa ba wai labari ba.

Na Farko:

Wata rana sun fita zagayen wa’azi a wasu jihohi, sai wayar Sheikh Abdullahi Bala Lau tafadi. Aka nemi wannan wayar ba’a gani ba.

Daga baya sai wata yarinya karama wacce ba musulma ba ta tsinci wayar, sai ta kaima mahaifiyar ta.

Malam yace, sun fita zasu tafi filin wa’azi da safe, sai wannan mahaifiyar yarinyar ta duba lambar karshe (last call) da aka kira a wayar, sai ta kira lambar. Suna kan hanyarsu zuwa filin wa’azi, sai wannan matar ta kira daya daga cikinsu, sai yaji muryar mace, kuma yaga baida lambar matar, kawai sai yakashe kiran.

Sai matar ta kuma kira, yana dauka sai tace wayar kuce tafa’di muka tsinta shine na kira in sanar daku.

Nan take hankalin manyan malamai yakoma sauraron abinda take fadi, dama ana tsaka da neman inda wayar take. Sai aka tambaye ta inda za’a sameta, sai tace yanzu haka tana cikin ECWA church dake garin mubi, jihar Adamawa kenan.

Nan take Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun yace tawagar wa’azi ta karkata a wuce ECWA church domin karbar wannan wayar.

Ana isa wajen chochi, sai matar da ita da yarinyar ta karama wacce ta tsinci wayar suka fito. Nan take suka bayarda wannan wayar, kuma ita mahaifiyar yarinyar tayi bayanin cewar, yarinyarta ce ta tsinci wannan wayar sai ta kawo mata.

Nan take, Malamai sukayi godiya akan abin arzikin da wadannan bayin Allah sukayi, sai Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun yafito da kudi yabaiwa yarinyar saboda jin dadin abinda ta aikata, sai mahaifiyarta tace a’a, su don Allah sukayi ba wai don a basu kudi ba.
…………………………..

Na Biyu:

Tawagar zagayen wa’azi yacigaba da aiki, har Allah yakaisu jihar Kano.

Aka gabatar da wa’azi acikin daya daga cikin Masallatanmu na Sunnah, ana idar da wa’azi lokacin Sallah yayi, aka gabatar da Sallah.

Ana idar da Sallah, sai wani mutum a uzurce hankalinsa a ta’she, yazo wajen liman yace “Liman don Allah kataimake ni ayi min cigayar wayata, yanzu aka dauka acikin masallacinnan”. Sai liman yace haba dan uwa, bakasan cewa babu kyau yin cigiya a masallaci bane? Kawo lambar wayar domin mu kira muji ko Allah zaisa rabon ka ne.

Nan take aka kira wayar tafara ringing, mutumin da ya dauke wayar sai yadauka, aka yi mishi sallama nan take ya amsa, liman yace mishi, wannan wayar yanzu mai ita yake sanar damu bai san inda take ba, don Allah ka kawo ta wajen liman domin a bashi wayarsa.

Wannan mutumin yace, “malam gaskiya kuyi hakuri, dama banida waya kuma na samu”.

Kai tsaye abinda yafadima Liman kenan, sannan yakashe wayar gaba daya ba’a sake samun shi ba.

Don Allah, kayi nazari akan wadannan ababai guda biyu da suka faru tsakanin wancan kirista da wannan musulmin, wanene ya aikata aikin da Musulunci yake so?

Prof. Mansur Sokoto, mni