Masallacin Goje Tumu: Masu Gayawa Kansu Karya Su Dena, Suyi Fatan Alkhairi Kawai

Masallacin Goje Tumu: Masu Gayawa Kansu Karya Su Dena, Suyi Fatan Alkhairi Kawai

Masallacin Goje Tumu: Masu Gayawa Kansu Karya Su Dena, Suyi Fatan Alkhairi Kawai

Bari na fara da rokon Allah SWT ya karbi wannan aiki daga Senator Mohammed Danjuma Goje a matsayin Sadaqatul Jariya, ya gina masa gida a aljannah, kamar yanda Yayi alkawarin hakan ta harshen ManzonSa (SAW), Ameen.

Tun kimanin wata guda data gabata, an yita kuche akan gudanar da wannan Masallacin, inda mabiya Dariqar Tijjaniya suka yita taya kansu murna cewa an basu ragamar gudanar da wannan masallaci, yayin da wasu kuma suka musa hakan, suna bayyana cewa maganar bata da tushe balle makama, salo ne kawai na intimidating wanda ya gina masallacin da kokarin sashi a angle ta yanda zai rasa mafita dole kawai sai ya basu.

A rubuce-rubucen yan Tijjaniyya da nayita karantawa, hujjar da suka dogara da ita cewa sune sukafi chance chanchanta a bawa wannan masallaci itace wai gidajen da Senator Danjuma Goje ya saya ya rusa ya kara da filin gidansu na gado ya gina masallacin, gidajen yan Darikar Tijjaniyya ne.

Wasu kuma suna karawa da cewa wai a lokacin da masu gidajen wajen suka sayarwa Sen. Goje gidajensu, anyi sharadin cewa dole ya yadda cewa zai bawa yan Tijjaniyya masallacin idan ya gina, kafun nan suka yarda suka sayar masa da gidajen nasu.

A wasu rubuce-rubucen kuma, wasu yan Tijjaniyya sun kara da cewa wai dukkanin kananan masallatai dake arean da masallacin yake masallatan Tijjaniyya ne. Naga wani rubutu da mai rubutun ke cewa wai anguwar da aka gina masallacin kusan dukkan mutanen anguwar ‘yaya ne da jikoki da kuma almajiran wani Shehunsu na Dariqa, saboda haka bai kamata a bawa yan Izala masallacin ba tunda basu da mutane a anguwar.

Bari mu dora wadannan maganganu akan mizanin Shari’ah da kuma hankali, muga ko zasu rike ruwa.

Da farko dai, bincike da nayi a anguwar ya tabbatar da cewa dukkan gidajen da aka tayar a wajen aka kara girman filin da aka gina masallacin gaba dayansu sayansu Goje yayi da kudi. Babu wanda ya bada gidansa ko filinsa kyauta. Ciniki akayi da kowa, aka tsadance, ya amince aka biyashi kudinsa LAKADAN. Saboda haka a mizanin hankali, ka sayarwa mutum guri, ya cire kudi ya baka, kasa hanu ka karba, sannan kuma ka dawo kace sai yanda kakeso zaiyi da abunsa to ba’ayi masa adalci ba.

Sannan bincike na ya tabbatar min da cewa babu wani sharadi da akayi tsakanin Senator Danjuma Goje da wadanda suka sayar masa da gidaje cewa idan ya kammala aikin masallacin zai bawa yan Tijjaniyya, babu wannan sharadin a rubuce, kuma babu wani cikin wadanda suka sayarwa Goje da gidajensu da yace anyi wannan sharadin dashi baki-da-baki.

Kuma mu kaddara ma anyi wannan sharadin a rubuce, to ko anyishi, sharadin bacecce ne a ma’aunin Shari’ar Musulunci. Annabi SAW ya fada cikin Hadisin Nana Aisha (RA) wanda Bukhari da Muslim suka ruwaito, Annabi SAW yace “Meye yake damun mutane ne suke sanya sharadi a cikin ciniki, sharadin da babu shi a cikin littafin Allah? Duk wanda ya sanya wani sharadi (a cikin ciniki) wanda babu shi a cikin littafin Allah to bacecce ne, koda sharadi guda dari ne.” Duk wanda ya karanta Fiqhun Musulunci yasan wannan ka’ida.

Sa’annan cewa wai kananan masallatai dake kewaye a sabon masallacin na yan Tijjaniyya ne, shima wannan koda ya kasance gaskiya ne bazai zama dalili na cewa dole a bawa yan Tijjaniyya masallacin ba, balle ma kuma ba haka abun yake ba, masallatan Ahlus Sunnah dake anguwar Herwagana sunfi na yan Tijjaniyya yawa nesa ba kusa ba.

Balle maganar cewa wai mutanen anguwar mafi yawancinsu ‘ya’ya ne da jikoki da kuma almajiran wani Shehun Tijjaniyya, wannan maganar kam ma babu wani wanda yasan anguwar Herwagana da zai saurareta.

Saboda tun farko masu taya kansu murna da godiya cewa an basu masallaci su kansu a cikin ransu sun san ba’a basu ba, kawai dai jamhuru ne na neman intimidating Goje.

Saboda haka duk wanda ya zagi Goje ko yaji haushinsa akan wannan mas’alar to wallahi alhakinsa kawai zai dauka, domin babu wata hujja gamsashiya ko guda daya data nuna cewa Goje ya musu alkawari, balle sure yanzu yazo ya karya alkawarin da yayi a baya.