MU KASANCE MASU ADALCI KO MUNA KIN MUTUM

 

MU KASANCE MASU ADALCI KO MUNA KIN MUTUM

Kadiyyar ricikin Isra’ila da Falasdinawa ya sa Manyan Malaman addinin Musulunci irinsu Sheikh Dr Idris Abdul-Aziz Bauchi da Sheikh Dr Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo sun yi magana, sun kawo tarihi da bayanai gwarwadon fahimtarsu (Allah Ya saka musu da alheri)

Kuma ni na saurari jawabin Malaman gaba daya, mu da Malaman duka ba a Kasar Falasdinu muke da zama ba, hakan na nufin mun tattaro bayanan mu ne daga hanyoyi dabam-dabam, dole a samu inda mukayi daidai da inda muka kuskure

Bayan jawabin Malam Idris da Malam Sani sai aka samu wasu munafukai suka kai gulmar Malam Idris zuwa ga Malam Sani cewa wai Malam Idris yace Hamas duk ‘yan shi’ah ne, wanda ba gaskiya bane sharri aka masa, amma sai Malam Sani ya fito ya yiwa Malam Idris raddi a fakaice har da kalmar zagi a ciki, amma bai kama suna ba

To daga bisani shima Malam Idris sai ya fito ya mayar wa Malam Sani raddi daidai da irin kalmomin da yayi amfani dashi a kansa, kuma har Malam Idris ya kammala mayar da raddinsa Malam Idris bai kama sunan Malam Sani ba

To sai na fara cin karo da maganganun wasu munafukai marassa adalcin cikin mu, suna zagin Malam Idris tare da bayyana cewa wai yaci mutuncin Malam Sani, to wannan magana munafurci ne, rashina adalci ne tsantsa, domin Malam Idris bai kama suna ba kamar yadda shima Malam Sani bai kama suna ba

Duk kiyayyar da kuke yiwa Malam Idris ya dai kamata ku zama masu adalci, kafin ku fara zagin Malam Idris ya kamata ku fara zagin Malam Sani kenan, tunda shi fara zagin Malam ba tare da ya kama suna ba yayi raddinsa a fakaice

Sannan ku sani cewa kafin Malam Sani ya shiga fagen karantarwa Malam Idris ya rigashi da shekaru masu yawa, sannan a shekarun haihuwa Malam Idris ya girmi Malam Sani nesa ba kusa ba, idan kuna da tarbiyya sai ku fara duba shekaru da kuma wanda ya fara hidima wa addinin Allah a tsakaninsu

Ba zamu hana duk wani munafuki ko masharranci zagi da cin mutuncin Malam Idris ba, kuma ba zamu iya hanaku yin kiyayya da Malam Idris ba, amma abinda muke so indai ku Musulmin kirki ne to shine ku masa adalci, adalci kuwa wajibi ne ba wai ganin dama ba, domin a wannan kadiyyar Malam Idris ba shi ya fara takalar Malam Sani ba, Malam Sani ne ya fara

Mu a irin tarbiyyan da aka mana, har wadanda ba Musulmai ba muna musu adalci, Shugaban ‘yan Shi’ah Ibrahim Zakzaky ya taba yin magana na gaskiya muka fito muka goyi bayansa muka bayyana ba sau daya ba, to wannan shine adalci ko kana kin mutum

Matsayin Malam Idris da Malam Sani duk daya ne a gareni, Allah shaida ne ina kaunarsu don Allah, kuma karantarwansu ya kwanta a raina, duk cikinsu babu wanda yake karban kudi a miyagun ‘yan siyasa, sannan ba Malaman Gwamnati bane, kuma ba Malaman fada bane, sannan su ba ‘yan kungiya bane da zasu boye gaskiya ko su ci amanar Musulmi, shiyasa a duk watan Ramadan nake yada Tafsirin Qur’ani da suke gabatarwa cikin groups dina na WhatsApp

Allah Ya saka musu da alheri, Ya karesu daga sharrin munafukai marassa adalci

Salaffiya ✍️

MU KASANCE MASU ADALCI KO MUNA KIN MUTUM - Salaffiya