HISBAH RUNDINAR ALLAH AIKIN KU NA KYAU

HISBAH RUNDINAR ALLAH AIKIN KU NA KYAU

‘Yar uwa saurara; inda matsalar take shine kaucewa karantarwan Musulunci da akeyi, Musulunci bai bar komai ba sai da yayi jawabi a kansa, musamman bayani akan mu’amalar mace

Mace itace ginshikin al’umma, idan ta gyaru al’umma ta gyaru, idan ta lalace al’umma ta lalace, shiyasa zaku ga Musulunci yafi bada muhimmanci wajen a kula da mace a bata tsaro sannan a tausaya mata saboda rauninta

A Musulunci laifi ne mace ta fita daga gida ita kadai taje wani guri ba tare da izni ba, ana so ma a hadata da muharrami yayi rakiya ko da kuwa aikin Hajji zata je, balle kuma ace ta fita ita kadai ta tafi gurin da ake aikata zina Iuwàdi da màd¡g0 wai taje sayan kifi, ku ji rainin wayo fa

Mata su zauna a gida shine rufin asirinsu, sai dai idan akwai wata lalura na neman ilmi, kasuwanci, ziyara, ibada ko aiki da zai sa su fita to wannan babu laifi amma da sharadin fitan, shiyasa har Allah Ya fada mana a cikin Qur’ani yace idan ta kama mata zasu fita daga gida to kar suyi fita irin na matan jahilan farko, wato kamar yadda matan mushrikai suke fita kafin bayyanar Annabi Muhammad (SAW)

Musulunci bai ce mace ta fita daga gida babu hijabi da muharrami ba, amma duk an kauce hanya shiyasa ake ganin ba daidai ba, Hisbah da shari’ah suke aiki da ilmi da hankali, don haka daidai ne su kama duk macen da ta fita daga gida zuwa guraren da ake aikata sabon Allah da fasadi

Musulunci mukeyi ba màgúzanc¡ ba, duk wani dan iska ko ‘yar iska da suke ganin Hisbah sun takura musu to su gudu su bar mana Kano su koma gidan bariki can jihar Lagos ko Abuja suyi yawo tsirara da karuwancinsu, amma Kano garin Musulunci ne cibiyar Arewa, sai an gyara tarbiyya, sai an kawar da fasikai

In ji a raina idan Allah ya bani iko duk wasu manyan ‘yan iska wakilan iblis masu lalata tarbiyya da aka daurewa gindi suna halakar da al’ummah; is either su tuba su dena, ko su gudu su bar gari, ko kuma na kawar dasu cikin sirri Wallahi, ba zan sa a kamasu ba, kawai za’a wayi gari ne aga suna yin baccin da babu farkawa sai a cikin kábar¡

Ina fata Hisbah su fadada aikinsu sosai, har sai matasa sun dena askin banza da shaye-shaye, duk macen da ta fita daga gida babu hijabi a kamata, ina da yakini Allah zai taimakesu

Daga karshe muna kira ga Gwamnonin mu na Arewa Musulmi don Allah ku karawa rundinar Hisbah karfin iko da albashi domin suyi aikinsu yadda ya dace

Yaa Allah Ka taimaki rundinar Hisbah ❤️ #HISBAH RUNDINAR ALLAH AIKIN KU NA KYAU - Salaffiya#Salaffiya