MAINENE WAYEWA?

MAINENE WAYEWA?

MAINENE WAYEWA? - SalaffiyaMAINENE WAYEWA?

1. Wayewa shi ne ka riƙe addinin ka da kyau.

2. Wayewa shi ne ka rike al’adun ka masu kyau.

3. Wayewa shi ne ka gane alkhairi ka aikata shi, kuma ka gane sharri ka guje shi.

4. Wayewa shi ne ka haɗa neman duniya da lahira, domin duniyar ka ta yi kyau, haka lahirar ka.

5. Wayewa shi ne ka zama mai kishin ƙasar ka da al’ummar ka.

6. Wayewa shi ne ka gane masoyinka da maƙiyin ka kuma ka iya zama da kowa.

7. Wayewa shi ne ka yiwa kanka shiri, domin ajiya maganin wata rana.

8. Wayewa shi ne ka iya aje komai inda ya dace, sanda ya dace, kamar yadda ya dace.

9. Wayewa shi ne ka auna magana kafin ka faɗe ta, ka zo kana nadama .

10. Wayewa shi ne Kasan za a mutu, kuma za a gamu da Allah, kuma zai yi hisabi, don haka ka fara yiwa kanka tun daga nan duniya .

11. Wayewa Shi ne ka rayu idan za ka iya, ba cuta ba cutarwa, kuma kada kayi abin kunya da zai dame ka nan gaba.

12. Wayewa ka shi ne ka yadda da yadda Allah ya yi ka, Kada ka rena kanka da baiwar da Allah ya yi maka.