KADA MU GAJIYA, GUDUMAWARMU GA ƳAN’UWANMU FALASƊINAWA SHI NE ADDU’A A ZAHIRI DA BAƊINI !!!

 

 

KADA MU GAJIYA, GUDUMAWARMU GA ƳAN'UWANMU FALASƊINAWA SHI NE ADDU'A A ZAHIRI DA BAƊINI !!! - SalaffiyaKADA MU GAJIYA, GUDUMAWARMU GA ƳAN’UWANMU FALASƊINAWA SHI NE ADDU’A A ZAHIRI DA BAƊINI !!!

A halin yanzu an tunkari kwanaki 20+ tun daga ranar 7/october/2023 ana fafata wannan yaƙin, waɗanda suke ikirarin ƙarfin mulki da ƙarfin soji (mayaƙa) da kayan yaƙi da goyon bayan ƙasashen duniya wanda suke ganin zasu iya shafe ƙasar Falasdinu cikin ƙanƙanin lokaci amma abin kunya har yanzu sun gaza yin hakan.

Wannan ke tabbatar da cewa Falasɗinawa Jarumai ne na yankan shakku waɗanda suka tsaya da ikon ALLAH, kuma duk waɗancan abubuwan da aka lissafo wanda abokan gaba suka mallaka basa girgiza su kuma kisan ƙare dangi da rauni ba shi ne nasarar yaƙi ba, nasarar yaƙi shi ne ka ƙwaci Ƴancinka koda za a ƙarar daku baki ɗaya.

Duk da kasancewar mafi yawan Labaran da muke bibiya ko muke karantawa suna zuwa mana da tsanani da zafi da raɗaɗi daga ɓangaren ta’addancin da ake yiwa ƴan’uwanmu falasɗinawa.

Sai dai a gefe guda bamu cika sanin halin da wancan ɓangaren Isra’ilawa suke ciki ba da lissafin yawan mutanen da aka kashe musu kuma aka jikkata, saboda Munafurci labarin ba ya samuwa sosai.

Wannan zai ƙara tabbatar mana da cewa suna amsar wuta daga sojojin turjiya domin yau da ace suna da wata nasara to da an bayyana Labaran nasararsu lungu da Saƙo na duniya.

Don haka Ya ƴan’uwa musulmai kada ku yi baƙin ciki kuma kada zukatanku su yi rauni, kada ku ɗebe ƙauna daga samun nasara akan abokan gaba, ku bada gudumawar addu’o’inku da ƙarfafawarku domin addu’o’inku tamkar makamai ne dake ɗaukaka kalmar ALLAH, bal ma dai Acikin Alƙur’ani Mai girma ALLAH (ﷻ) Ya ce:

وَلا تَهِنوا فِي ابتِغاءِ القَومِ إِن تَكونوا تَألَمونَ فَإِنَّهُم يَألَمونَ كَما تَألَمونَ وَتَرجونَ مِنَ اللَّهِ ما لا يَرجونَ وَكانَ اللَّهُ عَليمًا حَكيمًا٤٠١۝

Ma’ana: “Kuma kada ku yi rauni wajen neman mutanen; in kun kasance kuna jin raɗaɗi, to ai su ma (Kafirai) suna jin raɗaɗi kamar kuke jin raɗaɗi; kuma kuna fatan wani lada a wurin ALLAH, wanda su ba sa fatan irinsa. ALLAH kuwa Ya kasance Mai yawan sani ne, Mai yawan hikima.” [Nisa’i: 104]

Tsakani da ALLAH wannan ayar tana sanyaya min rai a ɓangaren yaƙin Falasɗinawa da Isra’ilawa, domin tana ƙara tabbatar mana ba mu kaɗai muke jin raɗaɗi ba.

Ya ALLAH ka girmama ladan Falasɗinawa ka basu nasara da ikon cin wannan jarrabawar, ka karɓi duk waɗanda aka kashe a matsayin shahidai.

  • Salaffiya ✍️

#SavePalastine
#IsraeliTerrorism