Babban Malami Prof. Muhd Sani Umar R/lemo Ya Fitar Da Sabon Littafi.

Babban Malami Prof. Muhd Sani Umar R/lemo Ya Fitar Da Sabon Littafi.

Babban Malami Prof. Muhd Sani Umar R/lemo Ya Fitar Da Sabon Littafi. - Salaffiya

LABARIN DALUTA DA JALUTA

 

Wannan Littafi mai Albarka wanda ya ke dauke da shafuka (140) ya kunshi Labarin Banu Isra’ila (Yahudawa) a lokacin da suka nemi Annabinsu da ya nad’a musu wani Jagora wanda zai jagorance su wajen yin Yaki. Inda Allah Ta’ala Ya ba mu Labarin Sarki Daluta da gwabzawarsu da Mayaki Jaluta, kamar yadda ya ke cikin Suratul Bakara, lambar Aya (246-252)

 

A cikin wannan Littafi an fito da “Darussa Na Shugabanci Da Siyasar Al’umma” in da Littafin ya kunshi matashiya daban-daban, kamar: Labarin Daluta Da Jaluta A Cikin Al-kur’ani, Zamanin Shugabancin Annabawa, Zamanin Shugabancin Alkalai, Bukatar Kare Rayuka Da Mutunci A Rayuwar Dan’adam, Cika Baki Ba Shi Ne Jarumta Ba, Allah Yana Bayar Da Mulkinsa Ga Wanda Ya Ga Dama, Duk Wata Hutacciyar Al’umma Ba Za Ta Iya Yaki Ba, Nasara Daga Allah Ta Ke, Ambaton Annabi Dawud A Cikin Alkur’ani, Jahilci Yana Hana Hango Ma’aunai Na Shari’a, Yadda Munafukai Su Ke Rusa Al’umma, Biyayya Ga Shugaba Hanyar Cin Nasara Ce, Komawa Ga Allah A Lokacin Tsanani, Allah Ya Kan Jarrabi Muminai. Da dai sauran bayanai masu yawa da Fa’idah.

 

Hakika wannan Littafi ya fito a kan Lokacinsa, lokacin da ake gumurzu tsakanin Yahudawa da Al’ummar musulmin Falasdinawa, haka nan Lokacin da al’umma ke cikin wani mummunan yanayi na rashin shugabanci nagari, da kuma kaucewa hanyoyin isa ga Nasara da samun bud’i daga tsanani.

 

Haka wannan Babban Malami abin koyi a cikin al’umma ya ke ta zuwa mana da abubuwan Alkhairi babu dare babu rana, babu abin da ya sanya a gabansa illa saita al’umma da nuna mata hanyar tsira da nusar da ita ga alkhairai. Karantarwa ta fatar baki babu dare babu rana, gina Malamai masu Da’awa da matasa masu tasowa a harkar ilimi, bayar da ingantattun fatawoyi ga al’umma masu dauke da zurfin bincike na ilimi da tsantseni da nufatar daidai.

 

Allah Ya kara wa Rayuwar wannan Babban Malami Albarka, Allah Ya jikan Mahaifa Ya saka musu da Alkhairi, Allah Ya kara masa Lafiya da Albarkar Rayuwa, Ya tsare mana shi.

 

Tuni an fitar da wannan Littafi, an rarraba shi ga Malamai da Daliban Ilimi Da Sauran Al’ummar Musulmi Kyauta saboda Allah.

 

Mai Rubutu:

Musa Muhammad Dankwano.

Sakataren Kwamitin Ilimi Na Dr. Muhd Sani Umar R/lemo (Hafizahullah)

23-10-2023.