KISAN-KAI! AKAN SIFANA NA KASHE DATTIJUWA DAMORI – ABBATI

KISAN-KAI! AKAN SIFANA NA KASHE DATTIJUWA DAMORI – ABBATIKISAN-KAI! AKAN SIFANA NA KASHE DATTIJUWA DAMORI - ABBATI - Salaffiya

Mustapha Adamu Isa (Abbati) wanda ƴansanda suka kama akan kisan wata dattizuwa a anguwar Jekadafari dake cikin garin Gombe, ya ce ya kashe matarne dan ta hanashi ɗaukar sifanan yin gyaran machine.

cikin yanayi na kuka, Abbati ya shaida min cewa “wani mutum ya kawo gyara da dare bayan mun tashi a gareji, na ɗauko sifana, sai marigayiyar tace ƙwace tace sam ba nawa bane in aje ta, sai na haƙura, bayan ta tafi gidanmu sai na koma ɗakinta ina binciken Sifanar, tana dawowa tace me nake nema, nace Sifanar da ta ƙwace tace in fita daga ɗakinta, Ni kuwa nace ba zan fita ba sai na ɗau sifanar, daga nanne muka fara taƙaddama har faɗa ta kaure tsakaninmu” in ji shi.

Ya ƙara da cewa “daga nan na yi amfani da wata wuƙa dake ɗakin marigayiyar wajen kasheta, duk da ita ta fara kuskurata da wukar” a cewarsa.

Abbati ya yi waɗannan bayanai a wannan Alhamis, lokacin da rundunar ƴansanda ta bawa manema labarai damar zantawa da shi, da wasu masu laifin da ta gabatar.

Matashin ya kuma tabbatar da cewa sharri ya yi wa Idris wanda tunda farko yace tare suka yi kisan. “Idris bai san komaiba, kawai na ambaci sunanshine saboda ya taɓa jawo aka koreni a gareji tsawon shekara ɗaya” in ji Abbati.

Matashin me shekaru 18 da haihuwa, ya nemi hukumomi su yi mishi sassauci, inda cikin kuka yace sam bai da niyar kashe dattijuwar.

Rundunar ƴansandan tace ta kamashine ta amfani da riga da wuƙar da ya yi kisan, inda ta gabatar da su ga manema labarai.

Salaffiya ✍️