WAJIBI NE MU BI SUNNAH SAU DA KAFA:

WAJIBI NE MU BI SUNNAH SAU DA KAFA

Sheikh Dr. Ibrahim Jalo Jalingo Hafizahullah

1. Wajibi ne al’ummar Musulmi su kasance masu bin sunnar Annabi mai tsira da aminci iya iyawarsu cikin Aqidah, da Ibadah, da kuma Mu’amalah.

2. Lalle hadithin Annabi mai tsira da amincin Allah shi ne sama da mazhabar ko wane malami, fiqhunsa kuma shi ne sama da fiqhun ko wane faqihi.

3. Bin mazhabar wani malami daga cikin Malaman Musulunci ba laifi ba ne matukar dai hakan bai kai mutum ga barin yin aiki da wani ingantaccen hadithin manzon Allah mai tsira da amincin Allah ba, in kuma ya kai shi ga barin yin aiki da wani ingantaccen nassin hadithin Annabi to lalle hakan ya haramta a bisa ittifakin Magabata.

4. To amma idan aka sami wata mas’ala da babu nassin Annabi mai tsira da amincin Allah a kanta to a nan dukkan wani malami mai ikon yin ijtihadi sai ya yi ijtihadinsa domin neman kaiwa ga hukuncin Shari’ah a cikinta, duk kuma hukuncin da ya samu kaiwa gare shi cikin ijtihadin nasa to da shi ne zai bauta wa Allah.

5. Shi kuma aammiy mara ikon yin ijtihadi irin na Ilmi sai ya yi koyi da wanda zuciyarsa ta fi kwanciya da shi cikin mujtahidan da suka yi ijtihadin Ilmi a cikin wannan mas’ala wacce babu ingantaccen nassin Manzon Allah mai tsira da amincin Allah a cikinta. Wannan shi ne abin da Shari’ar Musuluncin ta tabbatar.

6. Da wannan ne za a san cewa: wajibi ne a kan ko wane musulmi ya gina addininsa a kan sunnar Annabi mai tsira da amincin Allah; saboda duk wanda ya bar yin aiki da ingantaccen hadithin Annabi mai tsira da amincin Allah cikin wata mas’ala daga cikin mas’aloli kuma cikin zabinsa da jin dadinsa a bisa hujjar cewa: mazhabarsa ta saba wa hadithin, ko wata darikarsa ta saba wa hadithin, ko wani tsari na kungiyarsa ya saba wa hadithin, ko wani tsari na duniyarsa ya saba wa hadithin to lalle wannan ya bace ya bar hanyar Muminai; Wannan shi ne abin da nassoshin Alkur’ani mai girma da Sunnah mai daraja ke tabbatarwa.

7. Shaikhul Islam Ibnu Taimiyah ya ce cikin Majmuu’ul Fataawaa 24/202:-
‎((واما من تبينت له السنة فظن ان غيرها خير منها فهو ضال مبتدع بل كافر)).
Ma’ana: ((Amma wannan da Sunnah ta bayyana gare shi, sannan ya yi zaton cewa waninta ya fi ta alheri, to shi dan’bidi’ah ne, kai kafiri ne ma)).
Ya kuma ce cikin littafin 27/125:-
‎((ومن ترك النقل المصدق عن القائل المعصوم واتبع نقلا غير مصدق عن قائل غير معصوم فقد ضل ضلالا بعيدا)).
Ma’ana: ((Wanda ya bar nakalin da aka gaskata daga mai fada wanda yake ma’asuu’mi, sannan ya bi nakalin da ba a gaskata ba daga mai fadan da ba ma’asuu’mi ba, hakika ya bace bata mai nisa)).

8. Allah muke rokon Ya tausaya wa al’ummarmu Ya cusa musu ganin girman Annabi da son bin sunnarsa cikin zukatansu. Ameen.