Idan kaga mai Amsa sunan shi masoyin Shehu Ibrahim [RTA]

Idan kaga mai Amsa sunan shi masoyin Shehu Ibrahim [RTA]

Idan kaga mai Amsa sunan shi masoyin Shehu Ibrahim [RTA]
Amma ya cema Baya son Annabi [SAW] ko kuma baya kiyaye Dokokin ubangiji to kawai kaji Aranka dan hayaniyane ka fita sha’anin sa domin kawai da’awa son Shehu yake amma wallahi babu Shehu Aransa domin Barhama Niasse Babu abun da ya Shagala dashi kamar soyayyar mamzan Allah [SAW]

ma’abota Soyayya sunce duk mutumin da yake sonka zai kasance yana son abunda kake so kuma zai kasance yana kiyaye abun da masoyinsa bayaso saboda yana son faranta wa masoyinsa Ako da yaushe

mutumin da yadan faru da Soyayyar Shehu Ibrahim Niasse [RTA] to ya zama dole ya zama idan zaiki wani abu ya zama yana kinsa ne dan Allah. Badan wani abuba.

Dan Failar Shehu Yana ibada ne badan wuta ko aljanna ba Aa yana yine dan zatin Allah da neman yardarsa sannan yana neman ilimi ne dan Allah sannan ga Soyayyar Annabi [SAW] Azuciyar sa. Suna son iyalan gidansa da sahabbansa da Soyayyar Auliya’u domin waɗannan sune halayen jagoran mu Shehu Ibrahim Niasse [RTA]

Saboda haka kullun muka kasance muna rokan ubangiji ya ƙara tsarkake zuciyar mu bisa tafarkin son Shehu Ibrahim [RTA] domin idan mutum ya mutu akan tafarkin Failar ta haƙiƙa babu abun da zai hanashi shiga aljanna sai dai kawai idan bai mutu ba. domin idan kaga bai cika da kalman Shahadaba sai dai idan ba mutuwa yayiba wallahi.

Tabbas Shehu Ibrahim RTA yabar mana hanya mai kyau ga duk wadda yake nufin saduwa da Allah aransa. Allah ya qara muku tarakki Cikin Shehu Ibrahim [RTA]

SHEHU Ibrahim Niasse fardun nee ☝☝☝