Amfanin namijin goro, ga lafiya Dan Adam Amfanin sa. Guda goma sha shidda (16)

Amfanin namijin goro, ga lafiya Dan Adam Amfanin sa. Guda goma sha shidda (16)Amfanin namijin goro, ga lafiya Dan Adam Amfanin sa. Guda goma sha shidda (16) - Salaffiya
(1). Namijin goro yana maganin tari idan Aka hada da (TomTom) Ana chi.

(2). Namijin goro yana maganin matsalar ciwon sanyi, idan Aka hada da kanunfari A tafasa Asha Ruwan.

(3). Namijin goro yana maganin matsalar tsutsar ciki idan Aka jajjaga A matse Ruwan A Zuma Asha.

(4). Namijin goro Yana maganin ulcer idan aka hada da dabino Adaka, asa a Zuma A sha cokali biyu.

(5). Namijin goro Yana maganin Qara kuzari da nisan tafiya ga mai iyali idan Anaci da dabino daya namijin goro A tauna.
A Cinye kullun kaci sau uku.

(6). Namijin goro Yana gyara manyyi Idan Aka jajjaga A samu garin Hulba a Tafasa dashi Asaka a madaran Ruwa Asha.

(7). Namijin goro Yana kawar da majinar kirji idan kana cin shi.

(8). Namijin goro Yana hana shan Taba idan Aka hada da furan tumfafiya Ayi garin su Asamu Karan sigari da mutum yake Sha da madaran shanu wanda babu Hadi, Aciki ya kwana da safe kafin Aci komai a ba maishan Taban ya shanye duka bayan wasu minutes ko hours zaiyi duka Aman dattin Taban bazai kara jin sha’awar kara shan Taba ba.

(9). Namijin goro Yana maganin hawan jini, idan Aka hada ganyan cediya A tafasa Asa a Zuma Asha. Insha Allah yana magani

(10). Namijin goro Yana maganin ciwon kai. Idan kayi garin shi Ana hayaki Koda mace Mai yawan ciwon kai tayi. Insha Allah yana magani

(11). Namijin goro yana gyara murya idan kahada da danyar citta da Zuma kana dafawa da Lifpton kasha kafin kaci Komai da safe.

(12). Namijin goro Yana maganin kuraje Idan kasamu garin namijin goro ka kwaba da man zaitun. Idan kuma karzuwa ce ko bakon dauro ka kwaba da manja kashafa.

(13). Namijin goro Yana maganin sanyi Mara idan kahada da kanunfari da lemon tsami da Citta da garin Albabunaj.ka tafasa kasha da Zuma.

(14). Namijin goro Yana maganin wuta- idan kahada da sassaken itacen Qirya kadaka kasa gurin da wuta taci.

(15). Namijin goro Yana tsayar da jini idan kika hada da tsamiya ki tafasa Kisha zai tsaya. da izinin Allah

(16). Namijin Goro Yana kawar da wasu cututtuka da suke cikin mutum.

Wannan shine binciken danayi akan Namijin Goro Don Allah Katura Zuwa group 3

Allah ya kara mana lafiya da Imani da kwanciyar Hankali Duniya da Lahira

Salaffiya ✍️