Hakuri maganin zaman duniya
Maganin Zaman Duniya
Wani hamshakin attijiri ne aka yi a kasar Sin wanda ya mallaki kadarori masu dinbin yawa da makudan kudade. Wannan attijiri yana da direba wanda yake yi masa dawainiya ba dare ba rana. A kullum idan direban nasa ya zauna sai ya yi ta sake sake a cikin zuciyarsa yana cewa, duk wahalar da nake yi da mutumin nan ba ya ba ni hakkina. Idan ya mutu haka zan tafi da wahalar banza, bayan na kare rayuwata a hidimarsa. Ana haka, kwatsam! Sai maigidan nasa ya kwanta ciwo. Kafin wani lokaci ya ce ga garinku. Da aka yi makoki aka kare direba na jiran sallamarsa sai matar maigidan nasa ta kira shi ta ce, yanzu kam sai ka je ka nemo mana direba.
Gabansa ya fadi ras! Sannan ya ce, ranki ya dade ni ma ai zan iya ci gaba da aikina idan kin amince. Sai matar ta ce, ina! Ai kai ne za ka zama sabon maigidana. A cikin dan kankanen lokaci mutumin naka ya rikide ya koma maigida yana shan daular da tsohon maigidansa ya tara, tare da sabuwar amaryarsa. A nan ne watarana yake cewa, a da na dauka ni nake hidimar maigidana. Ban sani ba ashe shi ne yake yi min hidima.
Darussa:
– Hakuri maganin zaman duniya
– Sanin gobe sai lillahi – Da yawa wanda kake yi ma hidima ba ka sani ba shi ne hadiminka
– Kada ka raina mutum. Watakila gobe zai amfane ka
– Mu nemi Halas don mu tsira. Da yawa abinda muke tarawa na duniya ba ba mu za mu ci ba.
Professor mansur sokoto.