TSAKANIN RARARA DA BUHARI: WA YA BUTULCE?

TSAKANIN RARARA DA BUHARI: WA YA BUTULCE?TSAKANIN RARARA DA BUHARI: WA YA BUTULCE? - Salaffiya

Cece-kuce ya barke musamman a kafafen sadarwar zamani tun bayan bullar wani faifan bidiyo in da aka juwo shahararren mawakin siyasa Dauda Adamu Abdullahi Kahuru Rarara yana caccakar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Mawakin dai wanda ya kira wani taron manema labarai a Kano, a satin ya gabata, bayan sukar Buhari wanda a cewarsa kamin saukarsa daga mulki sai da ya damalmala Nijeriya ya lalata kome, ya kuma ce mulkin Tunubu na wata ukun nan yafi dukkan shekaru 8 din Buhari alheri.

Haka Kuma ya zargi Buharin da butulce masa da yunkurin ganin bayansa ta hanyar janye masa jami’an tsaro domin a kashe shi.

Sai dai a lokacin da mutane suka fi mayar da hankali a kan sukar da yayi wa Buharin, wasu masharhanta na ganin cewa ba Buhari kawai ya soka ba, kuma da alama ya fake ne da guzuma domin harbin karsana, a zahiri gwamanati mai ci yake so yayi wa jan kunne idan aka yi la’akari da wani bangaren na maganganunsa, kamar yanda ya fada a cikin hirar;

1. Har zuwa yanzu gwamnatin Tunubu bata gayyace shi Abuja ba.

Da aka tambaye shi amma ai an ga yana zuwa Abuja, sai ya ce ko gobe ma tun da safe zai tafi, amma idan yaje ba Asarok Villa yake zuwa ba, gidan da ya kama haya yake zuwa yana hutawa.

2. Haka kuma kamar yanda ya fada, ya ce duk abinda sabuwar gwamnatin Tunubu ke yi, har zuwa yanzu, ba’a tuntubarsa duk da cewa shi ne wanda yafi kowa bayar da gudummuwa wajen kawo Tunubu kan mulki .

3. Ya ce da za’a nada ministoci ba’a nemi shawararsa ba, duk da cewa shi ne yafi kowa sanin wadanda suka yi wahala a tafiyar, kuma shi karan kansa kamata ya yi ace an bashi wasu mukaman ya ba mutanensa, amma har zuwa yau ba’a bashi ko daya ba.

4. Ya ce lokacin da aka kona masa gida, da wurin sana’a Tunubu yayi masa alkawarin zai bashi kudi ya biya masu wurin da yake haya, Wanda mutane suka kona din, amma har.yanzu bai cika wannan alkawarin ba.

5. Ya ce yaje yana so ya ga shugaban kasa Bola Tunubu domin ya bashi wata shawara, amma.aka hana shi ya ganshi.

7. Yace an nada ministocin da mafi yawansu ma basu san shi ba, sai an ce masu shi ne wanda yayi waka kaza.

8. Daga karshe sai ya kulle da yi wa Tunubu kashedi, in da ya ce zai yi hakuri na dan wani lokaci ya gani, ko abubuwa za su sauya, amma dai ba zai yi wa gwamnatin Tunubu uzuri na lokaci mai tsawo kamar yanda yayi wa Buhari ba.

A lokacin da ake jira a gani ko Shugaba Tunubu zai dauki wannan barazana ta mawakin ko a’a, mutane da yawa suna da tambayoyin da suka gaza samo amsoshinsu, tambayoyin sun hada da:

DA GASKE APC DA BUHARI SUN YI WA RARARA BUTULCI ?

SHIN DA GASKE RARARA BAI SAMU ABINDA YA KAMATA YA SAMU A GWAMNATIN BUHARI BA?

SHIN GASKIYANE YA DACE A TUNTUBI RARARA KAMIN A NADA MINISTOCI ?

 

#Salaffiya