Inna liLlahi Wa Inna IlaiHi Raji’un
Inna liLlahi Wa Inna IlaiHi Raji’un
Copy Daga Khalid Mu’azu Izala
Mun wayi gari da babbar jarrabawa na rashin babban aminin Mahaifina, kuma Malaminsa, Malaminmu, Imam Saidu Abubakar
Imam Saidu shine limamin Masallacin Juma’an Izala na 2 dake Abuja Quarters a birnin Gombe, kuma ma’ajin kudi na kungiyar Izala reshen Gombe ta Kudu.
Ya kasance Malami ne daya kare rayuwarsa wajen jagoranci da karantar da addini. Tun yana da kuruciya yake karantar da addini har karshen rayuwarsa.
Mun samu albarkar karantarwarsa tun muna Islamiyya, shi ka karantar dani Izun Tabara (Suratul Mulk zuwa Suratu Nuh) a lokacin da muke aji 5 a makarantar Malja’us Sunnah na Bolari ta Gabas, kuma wannan wajen yana daga cikin guraren da haddata tafi karfi kuma nafi iya karantawa a cikin Alkur’ani mai girma. Kuma ya karantar damu Hadisi, Tafsiri, Fiqhu, Larabci, Sirah, da kuma Tauhidi.
Ya Allah ina rokonka ka jikan wannan bawa naka da rahama, ka karbi kyawawan aiyyukansa ka gafarta masa kusakuransa, ya Allah kasa aljannar Firdausi itace makomarsa.