HADARIN BID’A DA ILLAR BIDI’A A RAYUWA

HADARIN BID’A DA ILLAR BIDI’A A RAYUWA
HADARIN BID'A DA ILLAR BIDI'A A RAYUWA - Salaffiya
An karbo daga Amr bin Salamah (رضي الله عنه) yace: Muna zaune a bakin kofar Abdullahi bn Mas’ud (رضي الله عنه) kafin cin abinci, don in ya fito mu bi shi zuwa Masallaci sai. Abu Musa al-Ashari (رضي الله عنه) ya zo ya ce: “Shin Abu Abdurrahman ya fito?” Muka ce: “A’a.” Sai ya zauna tare da mu yana jiran fitowar sa, da ya fito, muka tashi gabadaya zuwa gare shi. Abu Musa ( رضي الله عنه ) ya ce: “Ya Abu Abdurrahman! Na ga wani abu a cikin Masallaci wanda na ki. Amma Alhamdulillah, abin da na gani ba komai ba ne sai alheri.”

Ya ce: “Mene ne?” Abu Musa ( رضي الله عنه ) ya ce: “Idan kana raye zaka gani”. Sai Abu Musa ya ce: “Na ga wasu jama’a suna zaune a da’ira suna jiran sallah. A kowacce da’ira akwai wani mutum kuma a hannunsu akwai kananan duwatsu sai ya ce: ‘Ku ce Allahu-Akbar sau 100’ sai su ce Allahu Akbar sau 100. Sai ya ce: ‘Ku ce la’ilaha illallah sau 100, sai su ce la ilaha illallah sau 100, sai ya ce: ‘Ku ce Subhanallah sau 100’ sai su ce SubhanAllah sau 100. Abdullahi bn Mas’ud (رضي الله عنه) ya ce: “To me ka ce da su?” Ya ce: “Ban ce musu komai ba, sai dai ina jiran ra’ayinka [ko umurninka].” Ya ce: “Don me ba ka umarce su da su qirga munanan ayyukansu ba [wato. Ku nemi gafarar ayyukanku], kuma ka lamunce masu cewa ba za su gaba rasa ko daya daga ayyukansu na qwarai ba? Sa’an nan ya tafi zuwa garesu, muka tafi da shi har sai da ya isa ɗayan waɗannan da’irar, sai ya tsaya ya ce: “Mene ne wannan abun da naga kunayu?” Suka ce: “Ya Abu Abdurrahman! Wadannan ba komai ba ne face kananan duwatsu da muke kirga su da su, suna cewa Allahu-Akbar, la ilaha illallahu da SubhanAllah.

Ya ce: “Ku lissafa zunubanku! (kana) Ina mai tabbatar muku da cewa ba za ku rasa komai na kyawawan ayyukanku ba! Ku yi hattara ya ku al’ummar Muhammad (SAW) ya akayi kukayi gaggawar halaka Ga mu Sahabban Annabinku masu yawa, a ko’ina kuma ga tufafinsa da basu tsufa [ba su bace] ba, kuma har kayan alwalarsa basu karye ba. Na rantse da wanda raina ke hannunSa, ko dai ku al’umma ce mafificiya wajen shiryuwa fiye da al’ummar Muhammad ( صلى الله عليه وسلم ) ko kuwa kuna bude qofar bata.”

Suka ce: “Mun rantse da Allah Ya Abu Abdurrahman, ba mu yi nufin komai ba sai alheri.” Ya ce: “Mutane nawa ne suke niyya mai kyau amma ba za su cimma abin da sukayi nufi ba. Lallai Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ba mu labari cewa: “Hakika akwai mutane masu karatun Alqur’ani amma ba ya wuce makogwaronsu.” Na rantse da Allah ban sani ba. Wataƙila mafi yawansu daga cikinku suke.

Sannan ya tafi. Amr bn Salamah (رضي الله عنه) ya ce: “Mun ga wasu daga cikin wadanda suke zaune a wadannan da’irar suna yaki ranar Nahrawan, tare da Khawarij.”

[Ad-Darimi a cikin Sunan sa, 1/79].

Rubutuwa Malam Munir Assalafiy