WASU SUN ƊAUKA CEWA YAWAN MABIYA SHIKE TABBATAR DA GASKIYAR SU !!!

WASU SUN ƊAUKA CEWA YAWAN MABIYA SHIKE TABBATAR DA GASKIYAR SU !!!WASU SUN ƊAUKA CEWA YAWAN MABIYA SHIKE TABBATAR DA GASKIYAR SU !!! - Salaffiya WASU SUN ƊAUKA CEWA YAWAN MABIYA SHIKE TABBATAR DA GASKIYAR SU !!! - Salaffiya

Saurara ita gaskiya ba da yawan mabiya take tabbata ba, Gaskiya tana tabbata ne da ƙarfin hujja, kuma ƙarfin hujjar gaskiya shike sa a bita amma fa ga ma’abota hankali.

Babban Malamin nan Sheikh Muhammad Salih Al-uthaymeen [Rahimahullah] Yake cewa: “Mu bada yawan mutane muke sanin gaskiya ba, a’a muna sanin gaskiya ne da dacewar Alkur’ani da Sunnah.”

Hakanan Babban Malamin nan Ibn Qayyim [Rahimahullah] Yake cewa: “Idan kasan cewar a hanyar gaskiya kake, kada ka damu da karancin mabiyanta, koda kai kadai ne bita kawai, amma hanyar ƙarya ka guje mata komai yawan mabiyanta.”

Ita Gaskiya bata bukatar ado tun digindigin da kwalliyarta take shawagi, a koyaushe Qarya ita ce kufayin da ake sauyawa salo daban-daban domin ta haska sai dai kuma duk yadda ta kai ga haske dole ne watarana ta dusashe.

Acikin Alqur’ani maigirma ALLAH (SWT) Yana cewa:

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اتَّقُوا اللَّهَ وَكُونُوا مَعَ الصَّادِقِينَ

.“Yaku da kuka yi imani kuji tsoron ALLAH, kuma ku kasance tare da masu gaskiya.” [Attaubah:119]

Manzon ALLAH (ﷺ) Ya ce: “Ita gaskiya tana shiryawar ne zuwa aiki nagari, aiki nagari kuma yana shiryarwa ne zuwa ga aljannah. Hakika mutum bazai gushe ba yana gaskiya har a rubuta shi mai gaskiya awajen ALLAH. Ita kuwa Qarya tana shiryarwa ne zuwa ga fajirci, Fajirci kuwa yana shiryarwa ne zuwa ga wuta. Hakika mutum bazai gushe ba yana karya har a rubuta shi maqaryaci awajen ALLAH.” [Bukhari da Muslim]

A wani hadisin kuma Manzon ALLAH (ﷺ) Yake cewa: “Na hore ku da gaskiya! Domin ita tana tare da aiki nagari ne su kuwa ayyuka ne na Aljannah. Kashedinku da karya! Domin ita tana tare da Fajirci ne su kuwa ayyuka ne na ‘Yan wuta.” [Ibn Hibban]

Ita Gaskiya dokin qarfe ce, babu mai hawanta sai ma’abocin ta. Hakanan dangantuwa da ita Gaskiyar mataki ne na samun nasara a rayuwar dan-adam. Fadin ta komai dacinta shine zai sa kayi mutunci a idon mutanen da suke da gaskiyar.

Hakika fadin gaskiya da dangantuwa zuwa gare ta yakan iya jefa ka cikin surutu da suka, amma duk da hakan ka fadi gaskiyar, kuma kada ka yadda ka fadi gaskiya don ka burge, kai dai ya zamanto ka fada ne don a fahimci gaskiyar.

Ya ALLAH ka tabbatar damu a hanyar gaskiya kuma ka nuna mana gaskiya ka bamu ikon binta, kuma ka kawar damu daga hanyar Qarya kuma ka nuna mana Qarya ka bamu ikon guje mata. (Ameen)

Salaffiya ✍️