SOCIAL MEDIA FALALA CE DAGA ALLAH!!!

SOCIAL MEDIA FALALA CE DAGA ALLAH!!!
SOCIAL MEDIA FALALA CE DAGA ALLAH!!! - Salaffiya
A Wannan Zamani ALLAH Ya Sauqaqa Mana Hanyoyin Yaɗa ilimi Musamman kafofin Sada zumunta ya kamata Musulmi Yayi Amfani da Wannan Dama Domin ya bar wata sadaqa jariyah wacce zata rinƙa binsa har bayan rasuwar sa

Brother ba dole saika zama malami kafin ka yaɗa ilimi social media ba
ko wa’azin wani malami ka yaɗa wani ya amfana kana da lada kuma baka san ina wannan lada zata tsaya ba domin a lokacin da ka yaɗa wani ilmi wani ya amfana da shi shima yaje ya yaɗa ko yayi aiki dashi wani ya gani ya ɗauka haƙiƙa kaima kana da lada

Abu Huraira ALLAH ya ƙara masa yarda ya rawaito daga Annabi tsira da amincin ALLAH su tabbata a gareshi cewa

Duk wanda yayi kira zuwa ga shiriya yana da lada kwatankwacin wa’inda suka bishi cikin wannan shiriya kuma ba za’a rage musu komai daga cikin ladansu ba wanda kuma yayi kira zuwa ga ɓata yana da zunubi kwatankwacin zunubin wa’inda suka bishi kan wannan ɓata ba za’a rage musu komai daga cikin zunubnsu ba
Muslim

Ya dace Musulmi ya kula sosai kan abubuwan da yake yaɗawa a social media
domin laifin ko ladan baga wanda ka tura masa kaɗai yake tsaya wa ba zaka iya tura wani abu mara kyau na saɓon ALLAH laifin yaci gaba da binka har ranan tashin Al’qiyaama haka nan zaka iya tura wani abu na Alkhairi ladan yaci gaba da binka har ranan tashin qiyaama sai a kula ya zamto abinda zamu faɗi ko zamu tura baya ƙunshe da tsaɓon Allah.
Inya zamto abinda zamu faɗi babu Alkhairi aciki toh shiru shi yafi mana alkhairi

Mallam Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum

#Salaffiya