Ko ka san cewa ƙasar FALASƊIN ita ce ƙasar da aka kira ta da ƙasar ANNABAWA!??

Ko ka san cewa ƙasar FALASƊIN ita ce ƙasar da aka kira ta da ƙasar ANNABAWA!??

01: Falasɗin ta kasance ƙasar Annabawan Allah, amincin Allah ya tabbata a garesu baki ɗaya.

02: Annabi Ibrahim (a.s) shine ya fara yin hijira zuwa ƙasar Falasɗin.

03: Allah Ta’ala ya tseratar da Annabi Lut (a.s) daga azabar da ta afkawa Mutanensa a ƙasar Falasɗin.

04: Annabi Dawud (a.s) ya rayu a wannan ƙasar, kuma ya gina masallaci a nan.

05: Annabi Sulaiman (AS) ya kasance yana zaune a ƙasar nan, kuma yana mulkin duniya baki ɗaya.

06: Annabi Musa (A.S) ya gaya wa sahabbansa game da wannan ƙasa da kuma shiga wannan gari mai tsarki (Falasɗin). Ya kira wannan gari da mai tsarki saboda kasancewarsa ya barranta daga shirka da kuma kasancewarsa ƙasar Annabawa.

07: Mu’ujizozi da dama sun faru a wannan gari, ciki har da haihuwar Annabi Isah ɗan Maryam amincin Allah su tabbata a gareta.

08: A lokacin da Mutanen Annabi Isa (AS) suka so su kashe shi sai Allah Ta’ala ya dauke shi zuwa sama daga Qudus (watau Jerusalem).

09: Ɗaya daga cikin alamomin tashin ƙiyama shine dawowar Annabi Isa (AS) duniya a wannan ƙasar.

10: Annabi Isa (AS) zai kashe Dajjal a wani waje da ake kira (Bab Lud) a wannan ƙasar.

11: Falasɗin ita ce ƙasar da za a tashe kowa, Allah ya yi masa hisabi.

12: Daga wannan birnin ne Yajuju da Majuju za su fito su yaƙi Mutanen duniya da hargitsa duniyar.

13: Bayan haka ƙasar Falasɗin tana da darajar kasancewarta ALQIBLA ta farko ta Musulmi bayan an wajabta salloli biyar. Daga baya aka umurci Annabi Muhammad (ﷺ) da ya juya fuskarsa daga Masallacin Aqsa na (Jerusalem) zuwa Ka’aba na (Makkah) yayin Sallah. Masallacin da wannan lamari ya faru har yanzu ana kiransa da sunan Masallacin (Al-Qibla).

14: Bayan haka kuma anzo da Manzon Allah (ﷺ) daga Makka zuwa BAITUL-MAQDIS (Jerusalem) kafin a dauke shi zuwa sama a daren Mi’iraji.

15: Dukan Annabawa sun yi sallah anan, bayan da Annabi Muhammad ﷺ ya jagorance su sallah. Shine yasa Falasɗin ta zama ƙasar dukkan Annabawa, (copied) Salaffiya